Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-16 16:56:59    
Ofishin jakadanci na kasar Sin a kasashen waje da Sinawa 'yan kaka gida sun ci gaba da bai da kudaden taimako

cri
Bayan da aka yi mummunar girgizar kasa mai karfin digiri 7.8 na ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin a ran 12 ga wata, ma'aikatan ofishin jakadanci na kasar Sin a kasashen waje da Sinawa 'yan kaka gida sun yada ruhun 'taimakawa duk wanda ya gamu da matsala', sun ba da kudaden taimako cikin kwazo domin ba da gudummowa wajen sake gina gidage da kuma kyautata zaman rayuwar mutanen da suke shan wahalar girgizar kasar. Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da aka samu, an ce, Sinawa 'yan kaka gida sun riga sun bai wa wuraren da ke shan wahalar girgizar kasar kudaden taimako da kayayyakin tallafi da yawansu ya kai kudin Sin yuan miliyan 160 ta hanyoyi daban daban.

A birnin Lagos na kasasr Nijeriya, wani Basine da ke tafiyar da wani masana'antu da ba ya so a ambaci sunansa ya ba da kudin taimako mai yawan dalar Amurka dubu 500. Ya bayyana cewa, Sinawa 'yan kaka gida suna kishin mahaifiyarsu kasar Sin sosai, abu mai muhimmanci shi ne ba da gudummowa domin fama da girgizar kasar da kuma gudanar da ayyukan ceto.(Tasallah)