Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-16 11:37:47    
Masauraron CRI sun nuna damuwarsu a kan girgizar kasa da aka yi a gundumar Wenchuan

cri
Bayan da aka yi girgizar kasa da karfinta ya kai digiri 7.8 bisa ma'aunin Richter a gundumar Wenchuan da ke lardin Sichuan a kasar Sin, bi da bi ne masauraron CRI da ke wurare daban daban na duniya suka fara mika wasiku da sakwanni ko Email don nuna jejeto ga mutanen da ke yankunan da bala'in ya shafa.Masauraro suna fatan mutanen da ke yankunan da bala'in ya shafa za su samu karfin zuciyar fuskantar wannan bala'i, kuma sun yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su bayar da gudumawar agaji ga kasar Sin. Haka kuma sun yi imani cewa, girgizar kasa ba za ta kawo matsala ga gasar wasannin Olympic ta Beijing ba.

Wani mai sauraro daga Nijeriya Baban gida ya bayar da wasika cewa, yayin da na ji labarin, mutane dubu 10 sun riga mu gidan gaskiya a cikin girgizar kasa, don haka ba za a iya siffanta irin halin da ke cikin zuciyata ba.

Masauraron Albania Abdul Razzed Kassamy ya bayyana cewa, ban da mummunan bala'in da ya auku, matakan da shugabannin kasar Sin suka dauka sun fi burge shi.

Masu sauraro daga Nijeriya da na Italy da na Brazil da na Pakistan da na Saudi Arabiya da na Afganistan da na Jamus da na Niger da na Hungary da na Vietnam da na Latvian da na India sun mika wasiku ga CRI, inda suka bayyana cewa, sun yi imani cewa, girgizar kasa da aka yi a Wenchuan ba zai kawo cikas ga gasar wasannin Olympic ta Beijing ba, za a shirya wasannin Olympic na Beijing cikin nasara.(Bako)