Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-16 10:52:39    
(Sabunta) Firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya yi furuci cewa yawan mutane da suka rasu a sakamakon girgizar kasa da aka yi a lardin Sichuan zai zarce dubu 50

cri
Firaministan kasar Sin Mr. Wen jiabao wanda ke jagorancin aikin ceton mutane a lardin Sichuan ya yi furuci cewa, zuwa ran 15 ga wata da karfe 2 da yamma, yawan mutanen da aka iya tabbatar da rasuwarsu a sakamakon girgizar kasa da aka yi a lardin Sichuan ya kai 19509, ana kyautata zaton cewa yawan mutanen da suka rasu zai zarce dubu 50. Dalilin da ya sa an yi wannan hasashe shi ne sabo da ya zuwa yanzu yawan mutane aka bar su a cikin gine-ginen da suka rugurguje ya kai dubu 20, tare da bacewar mutane da dama.

A gun taron bayar da umurni a kan aikin yaki da girgizar kasa da kuma ceton mutane da abin ya shafa na majalisar gudanarwa da aka yi a jirgin kasa a ran 15 ga wata da dare, Wen Jiabao ya furta cewa, fadin kasar da aka shafi a cikin girgizar kasa da aka yi a Wenchuan ta lardin Sichuan ya kai muraba'in kilomita dubu 100, kuma karfin digirin girgizar kasa ya zarce na girgizar kasa ta Tangshan da ta auku a shekarar 1976. Daga mummunan sakamakon da girgizar kasa ta kawo, wannan girgizar kasa ta kasance girgizar kasa mafi muni kuma ta shafi wurare mafi yawa tun da aka kafa sabuwar Sin.

Wen Jiabao ya bayyana cewa, dole ne dukkan mutanen kasar Sin mu yi kokari ba tare da kasala ba wajen aikin yaki da girgizar kasa da ceton mutane da bala'in ya shafa. Ran 16 ga wata da safe, yayin da yake zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, yanzu ana cikin lokaci mafi muhimmanci wajen ceton mutane, muddin dai akwai makoma, sai ya kamata mu yi iyakacin kokari, bai kamata mu bar aikin ceton mutane ba.

Ya zuwa yanzu, yawan sojoji da 'yan sanda da sojojin farar hula da suka shiga aikin yaki da bala'i da kuma ceton mutane ya zarce dubu 120, ran 15 ga wata, sojojin kasar Sin sun ceci mutanen da yawansu ya kai dubu 10, kuma sun yin aikin jiyya ga masu ji raunata dubu 13, kazalika kuma sun kwashe mutane da bala'in ya shafa da yawansu ya kai dubu 120 zuwa sauran wurare. Haka kuma hanyoyin da aka hada da Wenchuan da Beichuan watau hedkwatocin wurin da aka yi girgizar kasa sun sake soma aiki.

Ya zuwa ran 15 ga wata, kwamitin tsakiya na kasar Sin ya kebe kudin da yawansu ya kai biliyan 2.25 wajen yaki da bala'in.Yawan kudin karo-karo da kayayyaki da kasar Sin ta samu daga hukumar daban daban na duniya ya kai RMB biliyan 1.344.(Bako)