Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-16 10:29:00    
Mutane kusan dubu 20 sun mutu sakamakon bala'in girgizar kasa dake jihar Sichuan

cri
Hukumar ba da umurni don yaki da bala'in girgizar kasa ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta tabbatar da cewa, ya zuwa ran 15 ga wata da karfe 4 da yamma, mutane kusan dubu 20 sun mutu sakamakon bala'in girgizar kasa da ta auku a jihar Sichuan, kuma an yi hasashe cewa, yawan mutane da suka mutu sakamakon bala'in zai kai sama da dubu 50.

Yanzu, mutane masu ceto sun riga sun ceci mutanen da suka jikata fiye da dubu 60 daga yankunan da ke fama da bala'in. Mutane masu jikata nan an riga an ba su ceto cikin lokaci kuma zaunar da su cikin daidaici.

A ran 15 ga wata, firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ya isa gundumar Qingchuan da ke arewacin lardin Sichuan, wadda ta ke fi shan wahalar girgizar kasar. Ya gayawa mutanen da bala'in wahalar girgizar kasar ya galabata cewa, gwamnatin kasar ba ta manta da yankunan karkara da ke shan wahalar girgizar kasa ba. Za ta tabbatar da ba da isasshen abinci da ruwan sha da tantuna da magunguna, sa'an nan kuma, gwamnatin Sin za ta bayar da kudin alawas wajen sake gina gidaje.

Ran nan da dare, an riga an sake bude hanyar dake cikin yammancin gundumar Wenchuan, wadda za ta hada wurin tsakiyar girgizar kasa da sauran wurare. Hanyar nan za ta ba da tabbaci mai karfi ga aikin ceto a gundumar Wenchuan.

Kazalika kuma, ya zuwa ran 15 ga wata, ma'aikatar kudi na gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta riga ta ba da kudin agaji don yaki da bala'in girgizar kasa da yawansa ya kai kudin Sin Yuan biliyan 2.24. Kuma an samu kudi da kayayyakin agaji da yawan kudinsu ya kai kudin Sin Yuan biliyan 1.344 daga fannoni daban daban a dukkan fadin kasar. (Zubairu)