Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-15 15:16:23    
Kasashen duniya suna cigaba da bayar da agaji ga yankunan da bala'in girgizar kasa ya ritsa da su da nunawa kasar Sin jejeto

cri
Bayan da mummunar girgizar kasa ta yi barna a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, jiya 14 ga wata, gamayyar kasa da kasa suka cigaba da samar da tallafin kudi ko agajin jin-kai ga ayyukan yaki da bala'in da ayyukan ceto, kuma ta hanyoyi daban-daban ne suka nunawa gwamnatin kasar Sin da jama'arta jejeto da cikakken goyon-baya.

A halin yanzu, gwamnatin Amurka ta riga ta samarwa kasar Sin tallafin dala dubu 500. Jiragen saman jigilar kayayyaki guda biyu na kasar Rasha wadanda ke dauke da kayan agaji na jin-kai sun riga sun isa birnin Chengdu. Kazalika kuma, gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewar, za ta baiwa yankunan da girgizar kasa ta shafa kayan agaji da darajarsa ta kai pound miliyan guda. A nata bangare, gwamnatin Faransa ta yi nuni da cewar, za ta tura wani babban jirgin saman jigilar kayayyaki wanda ke dauke da kayayyakin agaji da darajarsu ta kai kudin EURO dubu 250 a gobe 16 ga wata. Mutanen bangarori daban-daban na kasar Japan su ma sun yi alkawarin bayar da tallafi ga yankuna wadanda suka yi raga-raga.

Bugu da kari kuma, wasu gwamnatocin kasashen duniya, ciki har da Belgium, da Italy, da Mexico, da Koriya ta Kudu, da Pakistan, da Indiya tare kuma da wasu kungiyoyin kasa da kasa kamar asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya sun bayar da agaji ga kasar Sin.

A waje daya kuma, cikin 'yan kwanakin nan, Sinawa 'yan kaka-gida, da daliban Sin daga kasashen Qatar, da Thailand, da Canada, da Amurka, da Australiya, da Afghanistan, da Philippines, da Mexico, da Indonesiya sun nuna matukar juyayi da bayar da babban taimako ga mutanen yankunan da mummunar girgizar kasa ta shafa.

Dadin dadawa kuma, kafofin watsa labaru na kasashen Koriya ta Kudu da Singapore bi da bi ne suka bayar da bayanai jiya 14 ga wata, inda suka yabawa gwamnatin Sin wajen tafiyar da ayyukan ceto. Shekaranjiya wato 13 ga wata, kafofin watsa labaru na kasashen Amurka, da Japan, da Australiya, da Birtaniya, da New Zealand, da Switzerland, da Malaysiya, da Jamus, da Thailand suka bayar da bayanai daya bayan daya, inda suka maida hankulansu sosai kan halin da ake ciki a gundumar Wenchuan, haka kuma, suka yabawa gwamnatin Sin wajen gudanar da ayyukan ceto.

A wata sabuwa kuma, an ce, shugabannin kasashen Kazakhstan, da Georgia, da Ukraine, da Iran, da Turkiyya bi da bi ne suka bugo waya ga shugaba Hu Jintao da firaminista Wen Jiabao na kasar Sin, ko ta sauran hanyoyi daban-daban, domin nuna musu jejeto, da nuna cikakken goyon-baya ga gwamnatin Sin da jama'arta wajen kokarin yaki da girgizar kasa da ceto mutane.(Murtala)