Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-15 14:21:13    
Rayukan jama'a sun fi kome daraja

cri
Jaridar "People's Daily" da aka buga a ran 15 ga wata ta bayar da bayanin edita game da aikin ba da agaji bayan aukuwar bala'in girgizar kasa a jihar Sichuan, inda ta ce, a cikin zuciyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamantin kasar, da zuciyar dukkan mutane masu ba da agaji, rayuwar jama'a sun fi kome daraja.

A cikin bayani, an ce, mutane da yawa sun mutu ko ji rauni sakamakon bala'in girgizar kasa da ya auku a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan. Ba da tabbaci ga rayukan jama'a dake cikin yankin bala'in, da kuma rage yawan mutane da suka mutu ko ji rauni, wannan ya zama abin mafi muhimmanci yanzu.

An ce, idan akwai wata 'yar dama, to ya kamata mu yi iyakancin kokarinmu, idan akwai wani mutun yana karkashin gine-gine da ya rushe, sai ya kamata mu yi iyakancin kokarinmu wajen ba da ceto.

Ban da wannan kuma, bayanin ya ce, ya kamata kwamitin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da gwamnatocin matakai daban daban su mai da rayukan jama'a a gaban kome, su aiwatar da dukkan ayyukan ba da agaji da ayyukan zaunar da masu shan wahalar bala'in, da tsara shirin ba da agaji, da kuma yi kokari tayar da himmar dukkan jama'a, don yin fama da bala'in girgizar kasa. (Zubairu)