Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-14 20:35:59    
Kasashen duniya suna samar wa kasar Sin taimakon kudi domin fama da bala'in girgizar kasa

cri

Bayan da aka samu bala'in girgizar kasa mai tsanani sosai a lardin Sichuan na kasar Sin, a ran 13 ga wata, bi da bi ne kasashen duniya suka bayyana cewa, za su samar da kudi da kayayyakin jin kai ga ayyukan fama da bala'in girgizar kasa da kasar Sin take yi.

Madam Dana Perino, kakakin fadar shugaban kasar Amurka ta sanar da cewa, kasar Amurka za ta samar wa kasar Sin taimakon kudi dalar Amurka dubu dari 5. Ta kuma bayyana cewa, bayan da aka samu cigaban binciken bala'in, bangaren Amurka zai yi la'akarin samar da karin taimakon kudi.

A waje daya kuma, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Norway ta sanar da cewa, gwamnatin kasar Norway ta tsai da kudurin samar wa kasar Sin taimakon kudin da yawansa zai kai dalar Amurka kimanin miliyan 3 da dubu dari 9. Sannan kuma, ministan kula da muhalli da neman cigaban kasashen Duniya Erik Solheim ya ce, idan bangaren kasar Sin yana bukatar kasar Norway da ta samar da injunan musamman ko sauran taimako, kasar Norway za ta yi namijin kokarinta bisa karfinta. (Sanusi Chen)