Ran 14 ga wata, a nan Beijing, Feng Zhenglin, mataimakin ministan harkokin zirga-zirga da sufuri na kasar Sin ya bayyana cewa, yanzu an riga an maido da sufuri yadda ya kamata a dukkan tagwayen hanyoyi a lardin Sichuan.
Ya kara da cewa, yanzu ana dora muhimmanci kan bude hanyoyin zuwa gundumar Wenchuan, wato cibiyar girgizar kasa a wannan karo. A wuraren da ke da nisan kilomita 50 a tsakaninsu da Wenchuan, tsaunuka sun sami rinjaye, wadanda kuma suka lalace sosai a sakamakon girgizar kasa, sa'an nan kuma, an yi ta samun kananan girgizar kasa, shi ya sa ana fama da babbar matsala wajen sake bude hanyoyin zuwa wannan gunduma.(Tasallah)
|