Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-14 17:38:33    
An riga an bude hanyar ceton rai zuwa Wenchuan

cri
Kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya ruwaito mana labarin cewa, yanzu an riga an bude hanyar ceton rai zuwa gundunar Wenchuan ta yankin Aba na kabilun Tibet da Qiang mai cin gashin kansa na kasar Sin, wadda ita ce cibiyar mummunar girgizar kasa a wannan karo.

Bayan da aka sami girgizar kasa a gundumar Wenchuan, hanyoyi sun toshe, wutar lantarki ta katse, kuma aikin sadarwa a wurin ya lalace, sa'an nan kuma, mazaunan wurin fiye da dubu 100 sun gaza tuntubar sauran wurare.

A ran 14 ga wata da tsakar rana, wata kungiyar aikin sadarwa ta rundunar soja ta kasar Sin a yankin Chengdu ta sauka gundumar Wenchuan daga jirgin sama mai saukar ungulu tare da wayar salula, ta haka halin da ake ciki a Wenchuan a harkokin aikin sadarwa ya sami kyautatuwa. Ya zuwa ran 14 ga wata da misalin karfe 8 da safe, sojoji fiye da 800 na kasar Sin suna gudanar da ayyukan ceto a Wenchuan. Karin sojoji suna kan hanyar zuwa Wenchuan.(Tasallah)