Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-14 11:50:48    
(Sabunta2)Labarun babbar girgizar kasa a lardin Sichuan

cri

A ran 13 ga wata, gwamnatoci da shugabannin kasashen waje da kuma jami'an kungiyoyin duniya sun aika da sakonnin nuna jejeto ga shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao da firayin ministan kasar Mr. Wen Jiabao, ko bayar da sanarwa, domin nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suke yi wajen yaki da bala'in girgizar kasa.

Bi da bi ne, shugaban kasar Zambiya, da mataimakin shugaban kasar, da kuma ministan harkokin waje na kasar suka nuna jejeto ga gwamnatin kasar Sin da jama'arta, sun yi imani cewa, kasar Sin za ta cin nasarar yaki da bala'in da sake gina kasa.

Ministan harkokin waje na kasar Afirka ta kudu yana fatan jama'ar da ke fama da bala'in za su iya maido da zaman rayuwarsu tun da wuri, gwamnatin kasar Afirka ta kudu suna son bayar da taimako ga kasar Sin.

Ban da su kuma, kasashen Korea ta arewa, da Vietnam, da Amurka, da kungiyar EU, da Jamus, da Faransa, da Australiya da dai sauransu sun nuna jejeto ga kasar Sin.

Kamfanonin watsa labaru na kasa da kasa sun mai da hankali sosai kan girgizar kasa da ta faru a lardin Sichuan na kasar Sin.

Kamfanonin watsa labaru na Amurka, da Japan, da Australiya, da Ingila, da New Zealand, da Switzerland, da Malasiya, da Jamus, da Thailand da dai sauransu sun bayar labarai da bayanai, inda suka yaba wa ayyukan ceto da gwamnatin kasar Sin da jama'arta suke gudanarwa.

Kasashen Rasha, da Japan, da Cambodia, da Thailand da dai sauransu sun bayar da kyaututtukan kudi da kayayyaki ga kasar Sin domin ayyukan ceto.

Daliban kasar Sin da ke karatu a ketare su ma sun dauki matakai cikin gaggawa, sun bayar da kyautattukan kudi da kayayyaki ga kasar Sin, domin taimakawa kasar Sin da ta ci nasarar yaki da babbar girgizar kasar a lardin Sichuan na kasar Sin.(Danladi)