Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 21:28:53    
Sabunta: Wurare dabam daban na kasar Sin sun ba da taimako ga wurin da ke fama da bala'i a lardin Sichuan

cri

Ran 12 ga wata da yamma, bayan an samun girgizar kasa mai tsanani sosai a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan, wurare dabam daban na kasar Sin sun ba da taimako ga wurin da ke fama da bala'i.

Kwamitin tsakiya na matasan kwaminis ta kasar Sin ya yi niyyar ba da RMB fiye da Yuan miliyan 14 ga wurin da ke fama da bala'i. A lardunan Sichuan da Guizhou, an riga an kafa kungiyoyin matasa masu sa kai domin tinkarar bala'in. Ya zuwa ran 13 ga wata da karfe 5 na yamma, Sinawa mazauna kasashen waje sun riga sun ba da taimakon kudi miliyan 65. Ban da haka kuma, dalibai da malamai na jami'o'in birnin Beijing suna kokarin ba da taimako ga wuraren da ke fama da bala'i ta hanyoyin ba da taimakon kudi da kayayyaki, da ba da jini.