Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 20:23:20    
Sin ta nuna godiya ga kasashen duniya da su samar da goyon baya da taimakon agaji ga yankunan lardin Sichuan masu fama da girgizar kasa

cri
A ran 13 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Qin Gang ya yi bayani a gun taron manema labarai, cewa bangaren Sin ya nuna godiya da kuma maraba da kasashen duniya da su samar da goyon baya da taimakon agaji ga yankunan lardin Sichuan masu fama da girgizar kasa.
Kuma Qin Gang ya bayyana cewa, bayan aukuwar bala'in girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin, dimbin kasashe da kungiyoyin duniya sun nuna jaje ga bangaren Sin ta hanyoyi iri daban daban, kuma sun bayyana cewa, suna son samar da goyon baya da taimakon agaji ga gwamnati da jama'ar Sin wajen fama da bala'in da kuma gudanar da ayyukan ceto. Kuma Mr. Qin ya ce, hukumomin da abin ya shafa na kasar Sin sun riga sun kafa hanyoyin tuntuba, ta yadda bangarorin samar da taimako za su iya tuntubar hukumomin kasar Sin yadda ya kamata.(Kande Gao)