Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 20:14:16    
Wani karamin kauyen masu kama kifi da ke gabar gabas ta kogin Lhasa

cri

In an tabo magana kan ni'imtattun wurare irin na kauyukan masu kama kifi a wuraren da aka fi samun ruwa, watakila yawancin mutane suna ganin cewa, sai a wuraren da ke bakin teku kawai, suna iya ganin wadannan kyawawan kauyuka. Amma yanzu zan gabatar muku da wani karamin kauyen masu kama kifi a bayan birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin kuma maras mafitar teku, wanda ke kan tudu.

Kauyen Junba yana kan gabashin gaba ta kogin Lhasa a bangaren kasa, yana kuma cikin inda kogin Brahmaputra da kogin Lhasa suka hadu da juna. Kauyen Junba na cikin muhalli mai kyau, inda kuma ake iya ganin ni'imtattun wurare da kuma dimbin tabkuna manya da kanana. Tun can can can da har zuwa yanzu, mazaunan wurin suna ciyar da kansu da kamun kifi. Shi ne kauyen masu kama kifi daya tak a jihar Tibet. Mazaunan kauyen sun yi shekaru fiye da 300 suna ciyar da kansu da kama kifi. Nagartacciyar fasahar saka kwale-kwale da fatan shanu da kuma kwale-kwalen fatan shanu masu sigar musamman ta kabilar Tibet sun zama al'adun kabilar Tibet daya tak da masunta suka samar, suna da dogon tarihi, suna kuma shan bamban da sauran al'adu.

Baya ga matsalar karancin ruwa da jihar Tibet ke fama da ita, muhimmin dalilin da ya sa kauyen Junba ya zama kauyen masu kama kifi kawai a jihar Tibet shi ne domin a jihar Tibet yawancin 'yan kabilar Tibet ba su cin kifi saboda suna bin addinin Buddha, sun mayar da tabkuna a Tibet tamkar tabkuna masu tsarki, za a gurbata wadannan tabkuna masu tsarki saboda ana yin wanka a cikinsu ko kuma cin kifayen da aka kama daga cikinsu. Amma bisa almara da ke yaduwa a kauyen Junba, 'yan kabilar Tibet da suka zama a kauyen Junba suna iya kama da kumawa cin kifi saboda samun amincewa da Ubangiji, wanda ya yafe laifuffukansu na cin kifi.

Saboda kauyen Junba na cikin inda koguna 2 wato kogin Brahmaputra da kogin Lhasa suka hadu da juna, shi ya sa ana iya samun albarkatun kifaye da yawa a nan, wadanda namunsu ke da dadin ci kwarai. Mazaunan wurin sun kirkira dimbin hanyoyin dafa kifaye domin sun dade suna ciyar da kansu da kifaye. In masu yawon shakatawa sun kawo wa wannan karamin kauye ziyara, baya ga wasu abincin gargajiya irin na kabilar Tibet, suna iya dandano abinci iri daban daban da aka dafa da kifaye.

Aikin kawo albarka na mazaunan kauyen Junba da kuma zaman rayuwarsu suna da nasaba da kama kifi sosai, har ma harkokin nishadi da su kan yi a zaman yau da kullum suna da nasaba da kama kifi.

Kazalika kuma, mazaunan wurin suna yin cinikin sarrafa kyawawan kayayyakin fatan shanu masu inganci kuma masu rahusa, wadanda masu yawon shakatawa na gida da na waje suke nuna sha'awa sosai kansu.