Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-13 16:15:38    
Har zuwa yanzu babu labarin mutuwar mutanen kasashen waje da ke yawon shakatawa a sakamakon girgizar kasa

cri

Ran 13 ga wata a nan birnin Beijing, wani jami'in hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin ya gana da wakilinmu, ya ce, har zuwa yanzu, ba a sami labari na mutanen kasashen waje da ke yawon shakatawa a sakamakon girgizar kasa da ta faru a lardin Sichuan ba. Yanzu hukumar yawon shakatawa ta riga ta fara aiwatar da shirin tinkarar matsalar yawon shakatawa cikin gaggawa, ta riga ta kafa kungiyar jagorancin ayyukan tinkarar bala'in girgizar kasa da kuma ba da agaji, kuma ta kafa kungiyoyi 6 domin ba da agaji, kuma suna shirya sosai domin ba da taimako ga mutane masu yawon shakatawa da suka kamu da bala'in girgizar kasa.

Yanzu, hukumar yawon shakatawa tana kokarin tarar da halin da mutane masu yawon shakatawa ke ciki, da sauran labarun da abin ya shafa, da sunayen kungiyoyi da mutane masu yawon shakatawa da ke wurin. Hukumar yawon shakatawa ta kasar Sin tana mai da hankali sosai kan halin mutane masu yawon shakatawa na ciki da waje ke ciki, da kuma ba da taimako gan musu cikin sauri, da kuma taimaka musu domin janye dakw wurin da ke fama da bala'i.