Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-12 21:23:24    
Ayyukan gyare-gyaren da ake yi ga fadar Potala da ke jihar Tibet ta kasar Sin

cri

Abun da kuke saurara muryar waka ce da ma'aikata suka rera lokacin da suke yin gyare-gyare ga fadar Potala da ke jihar Tibet ta kasar Sin. Ma'aikata suna aiki kuma suna waka lokacin da suke aza harsashin ginin da wani irin yumbun da akan yi amfani da shi lokacin da suke gina gidaje masu sigar musamman na kabilar Tibet. Cikin shekaru 20 da suka wuce, kullum ana rera wannan waka lokacin da suke yin gyare-gyere da kuma kyautata dakunan fadar Potala.

Fadar Potala tana tsakiyar birnin Lhasa, hedkwatar jihar Jibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin, wadda take da shekaru fiye da 1,300 da ginuwa, wadda kuma aka gina a kan tudu mafi tsayi bisa leburin teku na duniya, kuma gine-ginen fadar da kayayyakin tarihin dake cikin fada sun samu kariya mafi kyau. Fadar tana da fadin fiye da murabba'in mita dubu 400, muhimmin ginin fadar kuma yana da hawa 13.

Amma sabo da yawan shekarun da ginawarta, da dalilin tsarin fasalin ginin da kuma sauye-sauyen yanayi, shi ya sa fadar Potala tana ta lalacewa. Tun daga shekaru na 50 na karnin da ya wuce, musamman ma cikin shekaru 20 da suka wuce, gwamnatin Sin ta kara rubanya kokari don yin gyare-gyare ga fadar.

Daga shekarar 1959 zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta ware kudi a kowace shekara domin yin gyare-gyare ga fadar Potala, ban da wannan kuma a shekarar 1989 da ta 2002 ta ware makudan kudade don yin manyan gyare-gyare har sau 2 ga fadar. Mr. Qamba Kelzang, shugaban ofishin kula da harkokin gyare-gyare ga fadar Potala ya bayyana cewa, "Daga shekarar 1989 zuwa ta 1994, gwamnatin Sin ta ware kudin Sin wato Yuan miliyan 53 don yin gyare-gyare a karo na farko ga fadar Potala, musamman don ceton fadar daga hadarin rushewa. Daga baya wato daga shekarar 2002 zuwa yanzu, gwamnatin Sin kuma ta ware kudin Yuan miliyan 170 don yin gyare-gyare a koro na 2 ga fadar."

An ce, gyare-gyaren da ake yi a karo na 2 ga fadar Potala suna hade da fannoni 5, wato kara inganta harsashin gine-ginen da aka yi a tsohon zamani, da daidaita da kuma kyautata muhallin da ke kewayen fadar, da kyautata tsarin ba da wutar lantarki da bututun jan ruwa da aikin kwana-kwana da gudun faduwar gatarin aradu, da kafa tsarin duba ingancin gine-ginen fadar ta hanyar kimiyya kuma cikin dogon lokaci, da kyautata zane-zanen bangwaye. Mr. Jamyang, tsohon injiniya na kamfanin zane-zane na fasahar gine-ginen tarihi na birnin Lhasa ta jihar Tibet ya fara aikin gyare-gyaren fadar Potala tun shekaru 80 na karnin da ya wuce, ya tuna da cewa, "Na sha shiga ayyukan gyare-gyare da kuma kiyaye kayayyakin tarihi na fadar Potala da na sauran wuraren ibada na jihar Tibet. Duk wadannan kayayyakin tarihi suna da babbar daraja bisa matsayin kasa da na duniya, wadanda kuma gwamnatin kasar ta ware makudan kudade don yi musu gyare-gyare da kuma kiyaye su."

Bisa abubuwan da injiniyoyin da ke ayyukan gyare-gyare suka bayyana an ce, domin yin ayyukan gyare-gyare ga fadar Potala da kyau, cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, hukumar kayayyakin tarihi na kasar Sin da sassan da abin ya shafa na jihar Tibet sun kafa wata kungiyar kwararrun sassa da yawa ciki har da gine-ginen tarihi da yanayin kasa da tsare ruwa, wadda ta yi bincike da kimantawa kan dukkan gine-ginen fadar Potala gaba daya ta hanyar kimiyya kuma cikin tsanaki. Ka'idar da ake bi wajen ayyukan gyare-gyare ita ce, "A yi wa kayayyakin tarihi gyare-gyare don mayar musu da sigarsu ta zamanin da, kuma ba za a canja asalin tsarinsu ba."

Jihar Tibet tana daya daga cikin larduna da jihohi masu yawan kayayyakin tarihi na kasar Sin, cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, jimlar kudin da gwamnatin tsakiya da ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta suka ware ta kai kusan Yuan biliyan daya domin yin gyare-gyare da kuma bude gidajen ibada da ni'imomin wuraren ban sha'awa na tarihi da na addini wadanda yawansu ya kai fiye da 1,400. Bisa shirin da gwamnatin kasar Sin ta tsayar an ce, daga shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar za ta kara ware kudin Sin kusan Yuan miliyan 600 don yin gyare-gyare ga gine-gine 22 na kayayyakin tarihi da na wuraren ibada na jihar daga duk fannoni, wasunsu kuma za a fara yin su ne daga wannan shekarar da muke ciki.