Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-09 21:44:39    
Shugaban Sin ya isa birnin Osaka domin cigaba da rangadinsa a kasar Japan

cri
Shugaba Hu Jintao na kasar Sin wanda a yanzu haka yake ziyarar aiki a kasar Japan ya kammala rangadinsa a babban birnin kasar wato Tokyo yau 9 ga wata, ya isa birnin Osaka, domin cigaba da ziyararsa a kasar Japan cikin kyakkyawan yanayin bazara.

Yayin da yake Osaka, Hu Jintao zai gana da ginshikan yankin Kansai, da halarci liyafar maraba da bangarori daban-daban na wurin za su shirya masa.

Bayan da ya isa Osaka a wannan rana, shugaba Hu Jintao ya yi wata 'yar takaitacciyar ziyara a birnin Yokohama, inda ya gana da shugaban gundumar Kanagawa ta Japan Matsuzawa Shigefumi, da magajin garin Yokohama wato Nakada Hiroshi.

Shugaba Hu Jintao ya yi nuni da cewar, gundumar Kanagawa da birnin Yokohama sun yi mu'amala da kasar Sin cikin dogon lokaci. A cikin shekaru da dama da suka gabata, bangarorin biyu sun kara inganta hadin-gwiwarsu a fannoni daban-daban, ciki har da tattalin arziki, da cinikayya, da al'adu. Wannan dai ya kawo babbar moriya ga bangarorin biyu, haka kuma, ya taka muhimmiyar rawa wajen daukaka cigaban dangantakar dake kasancewa tsakanin kasashen Sin da Japan. Kazalika kuma, shugaba Hu Jintao yana fatan birnin Yokohama da gundumar Kanagawa za su bayar da sabuwar gudummowa ga bunkasuwar dangantakar cimma moriyar juna bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Japan.

Matsuzawa Shigefumi da Nakada Hiroshi sun bayyana cewar, nan ba da jimawa ba, kasar Sin za ta shirya gasar wasannin Olympics a birnin Beijing da taron baje-koli na kasa da kasa a birnin Shanghai. Suna fatan yin amfani da wannan zarafi mai daraja, domin karfafa hadin-gwiwa da dankon zumunci tsakanin Japan da Sin, da yin kokari ba tare da kasala ba domin ciyar da kyakkyawar dangantakar kasashen biyu gaba.(Murtala)