Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-09 16:24:45    
Hu Jintao ya gana da manyan mambobin hadaddiyar kungiyar 'yan majalisu da ke nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing ta kasar Japan

cri

A ran 9 ga wata da safe a birnin Tokyo, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao, wanda yake ziyarar aiki a kasar Japan, ya gana da manyan mambobin hadaddiyar kungiyar 'yan majalisu da ke nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing ta kasar Japan, wadda shugaban majalisar wakilai Mr. Kono Yohei yake shugabanta.

Mr. Hu ya ce, jam'iyyu daban daban na kasar Japan sun kawar da bambancin ra'ayoyinsu, sun kafa hadaddiyar kungiyar 'yan majalisu da ke nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing ta kasar Japan, wannan ya bayyana cewa, jama'ar kasar Japan sun yada ra'ayin Olympics, jama'ar kasar Japan suna da zumunci mai zurfi ga jama'ar kasar Sin.

Mr Hu ya ce, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan gasar wannanin Olympics ta wannan karo. Gwamnatin kasar Sin da jama'arta za su cika alkawarin da suka yi wa kasashen duniya, za su yi kokari sosai, domin gudanar da gasar wasannin da kyau bisa taimako daga babban iyali na Olympics.

Shugaban majalisar wakilai ta kasar Japan kuma shugaban hadaddiyar kungiyar 'yan majalisu da ke nuna goyon baya ga gasar wasannin Olympics ta Beijing ta kasar Japan Mr. Kono Yohei yana nuna kyakkyawan fatan alheri ga samun nasarar shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Danladi)