Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-09 16:12:43    
Gwamnatin jihar Tibet ta kasar Sin tana ta zuba kudade a kan ayyukan da jama'a suke bukata

cri

A cikin shekarun baya, yawan kudin da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta samar kan yankin Tibet ya yi ta karuwa, kuma aikin hidima ga jama'a ya sami cigaba, mutane na kabilu dabam daban da suke zama a kabilar Tibet suna jin dadin ayyukan da gwamantin tsakiya ta kasar Sin ta ke aiwatar da kudin baitulmali.

Bisa labarin da muka samu, an ce, makarantun da ke Tibet sun sami kyautatuwa sosai, gwamnati ta soke kudin litattafai da na makaranta da ya kamata 'yan makaranta su biyu, ban da haka kuma, ana ba da taimakon kudin zaman rayuwa ga 'yan makaranta a ko wane wata.

Jami'in hukumar harkokin kudi ta yankin Tibet ya bayyana cewa, tun shekara ta 2001 zuwa shekara ta 2005, yawan kudin taimakon da gwamnatin kasar Sin take bayarwa ga ko wane manomi ko makiyayi a ko wace shekara ya kai RMB Yuan 400, kuma yankunan da rediyo da TV ke iya yada shirye-shirye ya kai fiye da kashi 85 cikin 100, kuma an sami sakamako mai kyau wajen yin rigakafi da kawar da ciwon annoba da cututukan da ake kamuwa da su a Tibet. Daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2010, gwamnatin kasar Sin za ta samar da RMB Yuan biliyan 100 a yankin Tibet domin sa kaimi ga bunkasuwarsa.