Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-09 14:41:27    
Shugaba Hu Jintao ya halarci bikin bangaren kasar Japan na bude shekarar yin cudanya da sada zumunta tsakanin samari na kasar Sin da kasar Japan

cri

A ran 8 ga wata da yamma, an shirya bikin bangaren kasar Japan na bude shekarar yin cudanya da sada zumunta tsakanin samari na kasar Sin da kasar Japan a jami'ar Waseda ta birnin Tokyo. Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao, da firaministan kasar Japan Mr. Yasuo Fukuda, da kuma tsahon firaministan kasar Japan Mr. Yasuhiro Nakasone sun halarci bikin.

Mr. Hu Jintao ya bayyana cewa, ya kamata a fara sada zumunta daga zuri'a zuwa zuri'a tsakanin kasar Sin da Japan tun da kananan yara na kasashen biyu. Yana fatan samari na kasashen biyu su dauki alhaki na sada zumunta tsakanin kasar Sin da kasar Japan da aka danka hannunsu.

Mr. Yasuo Fukuda kuma ya ce, yana fatan bikin budewar nan a yau zai zama fara aikace-aikacen yin cudanya iri daban daban a tsakanin samarin kasashen biyu, kuma yana fatan aikace-aikacen nan za su sa kaimi ga jama'ar kasashen biyu da su kara fahimtar juna, kuma a samu zumunta cikin dogon lokaci.

Kazalika kuma, Mr. Yasuhiro Nakasone ya ce, kasashen biyu sun shirya aikace-aikace na shekarar sada zumunta tsakanin samari, wannan yana da amfani ga jama'ar kasashen biyu da su kara fahimtar juna, kuma zai sa kaimi ga su wajen hadin gwiwar abokantaka cikin dogon lokaci. (Zubairu)