Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 16:56:22    
Kwararrun kasashen waje sun bayar da bayanai don yin Allah wadai da abin da kasashen yamma suka yi a kan batun Tibet

cri
Kwanakin nan, wadansu kwararrun kasashen waje sun bayar da bayanai ko yin hira da manema labarai bi da bi, don yin Allha wadai da abin da kasashen yamma suka yi a kan batun Tibet, da kuma bankado makarkashiyar da wasu 'yan tsirarrun suka kulla don neman yancin kan Tibet.

Lokacin da babban edita na mujallar "China" na kasar Rasha Mr. Vinogrotschi yake hira da kafofin yada labaru a rubuce a ran 7 ga wata, ya bayyana cewa, shi kansa yana da sha'awa sosai kan Tibet, kuma yana fatan ya iya gabatar da Tibet ga masu karatu a kasar Rasha, amma wannan ya bukaci bincike mai zurfi kuma da hankali sosai. Ya ce, a shekarar bara, ya ziyarci Tibet, wuraren yin aikace-aikacen addini da shahararrun wurare masu ni'ima sun shaku cikin zuciyarsa sosai. A cikin zaman al'umma na zamani, kiyaye da kuma raya al'adu yana da wuya sosai, amma gwamantin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan aikin kiyayewa da raya al'adun Tibet.

Shuhen malami na jami'a mai suna "Universita Degli Studi Insubria" na kasar Italia Mr. Irene Affede Di Paola ya bayar da bayani a wata jarida a kwanakin nan, inda ya ce, don tabbatar da cikakken yankin kasa, ya kamata kasar Sin ta dauki matakai nan da nan, amma wadansu kafofin watsa labaru na kasashen yamma sun yada jita-jita a kan batun nan. A gaskiya dai, mutanen kasashen yamma kadan ne da suka fahimci tarihin Tibet, abin da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka yi makarkashiya ce don kawo wa kasar Sin baraka.

Shahararen masanin tarihi kuma shehun malami na jami'ar mai suna "Universita Degli Studi Di Urbino" na kasar Italia Mr. Domenico Losurdo kuma ya bayar da labari a Internet, inda ya yi amfani da tarihi da bayanai da yawa, don bankado makarkashiyar da wadansu kungiyoyin kasashen yamma suka kulla don kawo wa kasar Sin baraka. Ya bayyana cewa, wai batun Tibet, a gaskiya dai, wata gwagwarmaya ce tsakanin masu son kawo baraka da masu yaki da baraka, haka kuma tsakanin ci gaba da maras ci gaba. (Zubairu)