
Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya yi shawarwari da firaministan Japan Fukuda Yasuo a ran 7 ga wata da safe. Don zurfafa dangantakar kawo moriyar juna dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, shugabannin biyu sun tsara shirin bunkasuwar huldarsu bisa hangen nesa, da tabbatar da muhimman ka'idojin ba da jagoranci ga bunkasuwar huldar kasashen biyu da tsara manufofin yin hakikanin hadin gwiwa da muhimman fannonin da kasashen biyu za su yi a matsakaicin da dogon lokaci don tsai da tsarin huldar Sin da Japan ta samun dauwamammiyar bunkasuwa cikin dogon lokaci.

Kafin shawarwarin, Mr. Hu Jintao ya halarci bikin da sarkin Japan Akihito ya shirya masa don marhabi da shi, kuma ya gana da sarki Akihito.(Lami)
|