Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-07 09:55:10    
Hanya kawai da za'a bi ita ce daina aika-aikar kawowa kasasr Sin baraka, in ji bayanin Jaridar People's Daily

cri
Jaridar People's Daily ta kasar Sin ta bayar da wani bayani yau 7 ga wata, inda ta ce, hanya kawai da rukunin mabiya Dalai Lama za su bi ita ce daina duk wani yunkurin kawowa kasar Sin baraka ba tare da wani jinkiri ba.

Bayanin ya ce, kowa na da mahaifarsa, ciki har da masu bin addinin Buddah. Mahaifa tamkar gida ne ga kowane mutum har abada. Babban tudun Qingzang, gida ne na kabilu daban-daban na kasar Sin, ciki har da kabilar Han da ta Tibet. Tun shekaru aru-aru, Tibet wani yanki ne da ba za'a iya raba shi daga kasar Sin ba, wanda ke karkashin mulkin gwamnatin tsakiya ta kasar Sin cikin dogon lokaci. Wannan hakikanin tarihi sanin kowa ne na daukacin al'ummomin kasar Sin, ciki har da 'yan uwa na kabilar Tibet.

Bayanin ya kara da cewar, kiyaye mulkin kai na kasa da cikakken yankinta, babbar moriya ce ga al'ummar kasar Sin, dukkanin jama'ar kasar Sin suna adawa da duk wani yunkurin kawowa kasar baraka. Hakikanin tarihi ya shaida cewar, ko shakka babu, duk wata makarkashiyar kawowa kasar Sin baraka za ta sha kaye!

A waje daya kuma, bayanin ya ce, yin watsi da danyen aiki na kawowa kasar Sin baraka, da daina duk wani yunkurin kawowa kasar Sin baraka ba tare da bata lokaci ba, zai tabbatar da sahihancin rukunin mabiya Dalai Lama na kiyaye dinkuwar duk kasar Sin gaba daya da kare moriyar mutanen Tibet. Al'ummomin kasar Sin da na wajenta suna zura ido kan ko rukunin mabiya Dalai Lama za su iya tafiyar da ayyukan dinkuwar duk kasar Sin gaba daya bisa ga la'akari da makomar mutane Tibet ko a'a.(Murtala)