Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 10:40:20    
Batun Tibet batu ne da da nasaba da ikon mulkin kasar Sin

cri
A ran 6 ga wata, an buga wani bayani a kan jaridar "People's Daily" ta kasar Sin, inda aka nuna cewa, "batun Tibet" batu ne da ke da nasaba da ikon mulkin kasar kasar Sin.

Wannan bayani ya nuna cewa, a kwanan baya, lokacin da rukunin Dalai yake zantawa kan batun Tibet a birnin Seattle na kasar Amurka, ya tsaya tsayin daka kan matsayinsa na "bin hanya ta tsakiya". Amma ainihin ma'anar wannan "hanya ta tsakiya" ita ce "neman 'yanci kan Tibet", wato yana son balle yankin Tibet daga kasar Sin.

Wannan bayani ya kara da cewa, ma'anar "hanya ta tsakiya" ita ce, da farko dai, kafa "wani babban yankin Tibet", sannan kuma "neman ikon mulkinsa da kansa". Ma'anar "babban yankin Tibet" ita ce ana son hada da yankin Tibet na yanzu da wasu yankunan lardunan Qinghai da Gansu da Sichuan da Yunnan, inda 'yan kabilar Tibet suke zama yanzu. Kuma ana son kafa wani babban yankin kabilar Tibet da ba a taba ganinsa a tarihi ba. Jimlar fadin wannan babban yankin kabilar Tibet ya kai kashi 1 cikin kashi 4 daga dukkan fadin kasar Sin. Ma'anar "neman ikon mulkin Tibet da kansa" ita ce, gwamnatin tsakiya ba ta iya tura sojojinta a yankin Tibet ba. Yankin Tibet ya iya raya huldar diplomasiyya a tsakaninsa da sauran kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa. Sabo da haka, za a iya ganin cewa, ainihin ma'anar "hanya ta tsakiya" ita ce ana son canja matsayin doka na kasancewar yankin Tibet a cikin kasar Sin, kuma ana son musunta ikon mulkin yankin Tibet da ke cikin hannun gwamnatin kasar Sin.

Wannan bayani ya kara nuna cewa, bisa tarihi da halin da ake ciki yanzu, za a iya kara ganewa kan batun Tibet. Wannan batu yana da nasaba da martabar wata kasa, kuma yana da nasaba da ainihin moriyar jama'ar kasar Sin. Ko da yake ana tsammani batun Tibet yana da sarkakiya sosai, ko rukunoni iri daban daban suke kokarin tsoma bakinsu a kan wannan batu, kasar Sin ba za ta amince da wannan ba ko kadan, jama'ar kasar Sin ma ba za su yarda da a ci tudun dafawa ba a kan wannan batu. (Sanusi Chen)