Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 15:28:55    
Kauyen al'adun gargajiya na kasar Sin a birnin Shenzhen

cri

Birnn Shenzhen na lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin, yankin musamman na raya tattalin aziki ne na farko da kasar Sin ta kebe. Ma iya cewa, Shenzhen na matsayin karamar kasar Sin ne a fannin samun bunkasuwa daga dukkan fannoni bayan da kasar Sin ta yi gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen duniya. A birnin Shenzhen, akwai wani shahararren wurin yawon shakatawa, inda ake iya ganin kananan abubuwan da aka kera bisa ni'imtattun wurare da ke wurare daban daban a kasar Sin. Shi ne kauyen al'adun gargajiya mai suna kyakkyawan kasar Sin da ke birnin Shenzhen.

Kauyen al'adun gargajiya na kyakkyawan kasar Sin yana kusa da kyakkyawan gulf na Shenzhen. Wurin ajiye kananan abubuwa da ke cikinsa, wurin ajiye kananan abubuwa ne mafi girma a duniya a yanzu, inda kuma ake iya ganin kananan abubuwa mafi yawa da aka kera bisa ni'imtattun wurare. Fadin wannan wurin ajiye kananan abubuwa ya kai misalin murabba'in mita dubu dari 3. Ana ajiye wadannan kananan abubuwan da aka kera bisa ni'imtattun wurare kusan 100 bisa taswirar kasar Sin, wadanda suka wakilci ni'imtattun wurare na halitta da wuraren tarihi na al'adu mafi nuna sigogin musamman na kasar Sin.


1 2 3 4