Ran 6 ga wata, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sauka birnin Tokyo, hedkwatar kasar Japan, ta haka ya fara ziyarar aikinsa na kwanaki 5 a Japan bisa gayyatar da gwamnatin Japan ta yi masa. Shugaba Hu ya mayar da ziyararsa a wannan karo tamkar wata kyakkyawar ziyara ce domin inganta hulda a tsakanin Sin da Japan.
A filin jiragen sama na Haneda na Japan, shugaba Hu ya ba da jawabi a rubuce, inda ya ce, Sin da Japan muhimman kasashe ne na Asiya da kuma na duniya. Bunkasa huldar zumunci da kyakkyawar makwabtaka a tsakanin Sin da Japan cikin dogon lokaci ya dace da babbar moriyar kasashen 2 da kuma jama'arsu duka. Shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 30 da Sin da Japan suka daddale yarjejeniyar shimfida zaman lafiya da sada zumunci a tsakaninsu. Kasashen 2 na fuskantar sabuwar dama wajen raya huldarsu. Ya kuma kara da cewa, yana fatan ta hanyar ziyararsa a wannan karo, kasashen 2 za su kara amincewa da juna ta fuskar siyasa da inganta zumunci a tsakaninsu, da kyautata hadin gwiwa da tsara shirin nan gaba, ta haka za su bude sabon shafi a fannin raya hulda a tsakaninsu domin moriyar juna daga fannoni daban daban bisa manyan tsare-tsare. Shugaban Sin ya ci gaba da cewa, tabbas ne zai tabbatar da makasudinsa na kai wa Japan ziyara a karkashin kokarin da bangarorin 2 suke yi.(Tasallah)
|