Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-06 10:17:57    
Mr. Hu Jintao ya bar Beijing don kai wa kasar Japan rangadi a kyakyawan yanayin bazara

cri

Bisa gayyatar da gwamnatin kasar Japan ta yi masa, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya bar birnin Beijing a ran 6 ga wata da safe, ya tafi birnin Tokyo don kai wa Japan rangadi na kwanaki 5.

Wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai wa Japan ziyara bayan shekaru 10 da suka wuce, kuma ita ce ziyarar farko da Hu Jintao ya yi bayan da ya sake zama shugaban kasar. A kwanakin baya, a yayin da Hu Jintao ya gana da kafofin yada labaru na Japan dake birnin Beijing, ya furta cewa, wannan ne wani rangadin sada zumunta.

A lokacin ziyararsa, Mr. Hu Jintao zai gana da sarkin Japan Akihito, zai yi shawarwari da firaministan Japan Fukuda Yasuo, kuma zai yi musanyar ra'ayi da jami'an majalisar ministoci da shugabannin jam'iyyu da mutanen da suka fito daga sassa daban daban na kasar Japan.(Lami)