Yau 5 ga wata, an ci gaba da yawo da fitilar wasannin Olympics a lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin, kuma gaba daya aka kammala yawon a zanguna biyar da ke birane uku.
Yau rana ce ta biyu da ake mika wutar wasannin Olympics a babban yankin kasar Sin, kuma masu mika wutar wasannin Olympics 208 sun mika wutar daga garin Wuzhishan zuwa garin Wanning har zuwa garin Qionghai, inda kuma aka ratsa wasu shahararrun wurare. Sabo da haka, yau aka fi ratsa garuruwa da zanguna wajen mika wutar wasanin Olympics. (Lubabatu)
|