Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 16:31:36    
Kungiyar WHO ta ce cutar boru ba za ta kawo mummunan tasiri ga wasannin Olympics na Beijing ba

cri

Ran 4 ga wata, Mr. Hans Troedsson wakilin kungiyar kiwon lafiya ta kasashen duniya wato kungiyar WHO da ke kasar Sin ya nuna cewa, cutar boru, wato cutar da ke kawo baki da kafafun shannu da ta bulla a wasu wuraren kasar Sin ba za su kawo mummunan tasiri ga wasannin Olympics na Beijing ba.

Mr. Hans Troedsson ya ce, babu wata shaida za ta iya nuna cewa, kwayoyin cutar EV71 wadda take hadassa cutar boru ta riga ta yadu. Yana tsamani, cutar boru ba za ta kawo matsala ga wasannin Olympics na Beijing da ko wane ayyukan da za a yi. Gwamnatin kasar Sin ta riga ta dauki matakai a zahiri, kuma ta riga ta gabatar da halin da ake ciki ga hukumar lafiya ta duniya, wato WHO.

Bisa labarin da muka samu, an ce, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta riga ta kafa hukumar yin rigakafi da kawar da cutar boru, ta haka domin jagoranci ayyukan wurare dabam daban.