Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 15:29:59    
Madam Serehlen, 'yar kabilar Mongoliya da ke da kanti kuma mai farin ciki

cri

A cikin shirinmu na yau, za mu kai ku babban filin ciyayi na Xilingul na jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ke arewacin kasar Sin inda za mu bakunci wata mai kantin sayar da tufaffi wato madam Serehlen don ganin yadda take zaman jin dadi a can tare da iyalinta.

Da wakilinmu ya shiga cikin wata karamar ma'aikatar dake wani titin dinkin tufafi na gundumar yammacin Uchumcin dake gabashin yankin Xilingul, ya ji karar kekunan dinki da muryar waka, an gaya masa cewa, za a isa ma'aikatar dinkin tufafi ta Serehlen.

Da wakilinmu ya je wajen kofar ma'aikatar dinkin tufafi, ya ga madam Serehlen, shugaban ma'aikatar da ke tsaye a gabansa gajeriya ce, wadda take saye da tufaffi masu halayen musamman na kabila wadanda kuma ta dinka ita da kanta, tana murmushi kuma tana cike da imani ga kanta. Da ganin haka ba wanda ya yi tsammani cewa, yau da 'yan shekaru da suka wuce, ita mai kiwon tumaki ce, ko da yake yanzu tana da ma'aikatar dinkin tufafi ta kanta, amma har ila yau tana nuna kaunar zuci ga zaman rayuwar makiyaya da ta yi a wancan lokaci. Ta ce,

"A da lokacin da nake shiyyar filin kiwo, yanayi yana da kyau, ana yin ruwan sama da yawa, mun yi kiwon tumaki da shanu a wancan lokaci, kuma zama rayuwarmu yana da dadi sosai."

A wancan lokaci, ya kasance da mutane 7 cikin iyalin Serehlen, kuma suna da filin ciyayi mai fadin fiye da kadada 260, da shanu da tumaki fiye da 300, ko da yake ba su yi arziki sosai ba, amma ba su damuwa da abinci da sutura. Amma daga baya, yanayin ya yi sauye-sauye, wato an kara dumamar yanayin duniya, kuma yawan dabbobin da ake kiwo a filin ciyayi sai kara karuwa yake, kuma kwararowar hamada da aka yi a babban filin ciyayi na Xilingul tana ta kara tsanani a kowace rana, shi ya sa hukumar yankin Xilingul ta kaddamar da muhimman tsare-tsare domin kyautata halittu masu rai da ke filin ciiyayi, daya daga cikin matakan da aka dauka shi ne daukar manoma da masu kiwo daga shiyyoyi masu mummunan yanayi zuwa cikin birane da garuruwa, kuma su juya hankulansu musamman kan ayyukan da ake yi cikin birane da garuruwa. Sabo da haka kuma iyalin Serehlen shi ma ya yi kaura a shekarar 2000 daga garinsu zuwa gundumar yammacin Uchumcin, sun fara sabon zamansu a nan. Madam Serehlen da kanwarta sun yi hayar wani gida a wani titin yin tufafi inda suka fara aikin dinke-dinke, ta tuna da cewa,

"A farkon zuwanmu a nan, ba mu saba da raman rayuwar da ake a a nan ba, a da ba mu kashe kudi domin dafa abinci da dumama daki da dibo ruwa, kome namu na karfin kanmu ya ishe mu. Amma yanzu a cikin birnin, ko kuna wuta domin dumama daki ko kuma samun ruwan sha, kai dukkan abubuwan da muke yi suna bukatar biyan kudi, ko yin tafiya wato yin sufuri ma yana bukatar biyan kudi."

Bayan 'yan shekarun da suka wuce, yanzu kantin dinkin tufafi na wadannan 'yanuwa mata 2 yana samun bunkasuwa sannu a hankali, ma'aikatar tana da dakuna 2, daya na dinkin tufafu, dayar kuma na sayar da tufafi ne. Bayan da aka yadada girman ma'aikatar kuma ana bukatar samun mutane don ba su hannu wajen aikin, kuma sun dauki yaran masu kiwo wadanda suka yi kaura zuwa nan tare da su cikin ma'aikatar. Yanzu yawan ma'aikata da ke cikin ma'aikatar dinkin tufafi na madam Surehlen ya riga ya karu har ya kai 15, kuma dukkansu sun zo ne daga makiyaya. Budurwa Dalanbajar tana daya daga cikin su, ta ce,

"Bayan da na zo nan, zaman rayuwata ta yi manyan sauye- sauye, wato na farko na koya fasahar dinkin tufafi, na 2 kuma na samu albashi, na iya ciyar da kaina. Ina nuna godiya sosai ga mai gidanmu wato madam Serehlen, wadda ta koya mini duk fasahar gaskiya ba tare da rage kome ba, sabo da haka na yi farin ciki kwarai."(Umaru)