Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-05-05 12:07:06    
Fitaccen mutum mai yin fim na kamfanin Hollywood na kasar Amurka Chris D.NeBe ya bayyana cewa zai nuna ainihin halin da Tibet ke ciki ga dukkan duniya

cri
Yayin da babban direktan kamfannin fim na Hollywood na Monarex na kasar Amurka Chris D.Nebe yake zantawa da manema labaru a nan birnin Beijing, ya bayyana cewa, yana fatan kaiwa Tibet ziyara tun da wuri, don nuna wa duk duniya ainihin halin da Tibet ke ciki.

Yanzu Chris D.NeBe yana shirya daukar fim "Tibet" watau daya daga cikin finafinai "kasar Sin mai ban al'ajabi". Ya riga ya gama daukar fim 4 da ke cikin dukkan finafinai "kasar Sin mai ban mamaki" kuma ya sami lambar yabo da yawa a duniya.

Mr D.Nebe ya bayyana cewa, rahotannin ba na gaskiya ba da wasu kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya suka bayar ba su yi adalci ba ga kasar Sin, a sa'i daya, ya bayyana mana cewa ba su fahimci kasar Sin ba.

NeBe ya bayyana cewa, yayin da mutanen kasar Sin suka cikin murna da annashuwa wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing, bai kamata a shafe bakin fenti ga gasar wasannin Olympic mai tsarki ba.(Bako)