Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-29 21:25:06    
An mika wutar yola ta wasannin Olimpic a birnin Phingyang

cri

Jama'a masu karantawa, a ranar 28 ga wannan wata da yamma (agogon wurin)an kammala mika wutar yola ta wasannin Olimpic na Beijing na shekarar 2008 a birnin Phingyang, hedkwatar kasar Korea ta Arewa. Wannan ne tasha ta 18 da aka mika wutar yola ta wasannin Olimpic na Beijing a kasashen ketare, kuma karo na farko ne da aka mika wutar yola a cikin Korea ta Arewa.

Brinin Phingyang da ke cikin watan Afril na cike da halin yanayin bazara sosai, wutar yola ta wasannin Olimpic da ta sauka birnin ta sa jama'ar Phingyang sun yi farin ciki sosai da sosai. A duk tsawon lokacin mika wutar yolar, mazaunan birnin Phingyang masu son bakunci da Sinawan da ke aiki ko dalibta a kasar Korea ta Arewa sun toshe hanyar da wutar Yala ta ratsa da ke da tsawon kilomita 20.

Da karfe 10 na safiyar wannan rana, tare da amon wakokin kasa na kasashen biyu wato Sin da Korea ta Arewa ne, an soma mika wutar Yola a birnin Phingyang. 'Yan kallo fiye da dubu goma sun taru a filin hasumiyar babban tunani da za a soma tashi daga nan don mika wutar yola, kuma sun jinjina furanni da tutocin kasashen biyu Sin da Korea ta Arewa, kuma sun daga kyalayen da aka rububa kalmomin da cewar "zumuncin da ke tsakanin kasar Sin da Korea ta Arewa" da "maraba da zuwan wutar yola ta wasannin Olimpic na Beijing a birnin Phingyang" da "birnin Beijing, ka kara karfi! wasannin Olimpic ma kara karfi! Da sauransu don murnar mika wutar yolar wasannin Olimpic a birnin Phingyang.

Wani mazaunin birnin Phingyang mai suna Park Yeng Cel ya gaya wa manema labaru cewa, tun daga lokacin da na sami labarin da za a mika wutar yolar wasannin Olimpic a birnin Phingyang sai na sa ran alheri ga zuwan ranar nan.

Maraba! Maraba! Maraba! birnin Beijing, ka kara karfi! Birnin Phingyang da wasannin Olimpic ma kara karfi!

Jama'a masu sauraro, kirarin nan shi ne kirarin da daliban kasar Sin da ke dalibata a birnin Phingyang suka yi domin zuwan wutar yola a Phingyang da kuma kara karfin kirari ga wasannin Olimpic. Wani dalibin kasar Sin ya burge sosai, kuma ya gaya wa manema labaru cewa, daga burge sai burge! na yi alfahari da sa ran alheri ga wasannin Olimpic a birnin Phingyang, ina fatan wasannin Olimpic na beijing zai sami cikakiyyar nasara! Birnin Beijing, ka kara karfi! Kuma birnin Phingyang ma kara karfi.

Da wutar yola ta zuwa hasumiyar da ke almanta zumuncin da ke tsakanin jama'ar kasashen biyu Sin da Korea ta Arewa, sai mai daukar wutar yola ta Korea ta Arewa mai suna Zung Myong cel ya mika wutar yola ga mai daukar wutar yola ta kasar Sin kuma jakadan kasar Sin da ke wakilci a Korea ta Arewa Mai suna Liu Xiaoming. Mr Zung Myong Cel ya gaya wa manecma labaru cewa, Ga ni wani ma'aikaci ne na Korea ta Arewa, da na yi tunani da lokacin da na mika wutar yola, sai na yi farin ciki sosai. Zumuncin gargajiya da ke tsakanin kasashenmu biyu zai kara karfi .

Wani jami'in kwamitin wasannin Olimpic na kasar Korea ta Arewa ya fayyace cewa, yawan mutanen birnin Phingyang da suka fito don je kallon mika wutar yolar wasannin Olimpic ya kai dubu 400, a ko'ina da wutar yola ta isa, sai ta sami maraba sosai daga jama'ar birnin Phingyang da ke gefunan hanyar da wutar ke ratsawa, kamar yadda jakadan Sin da ke kasar Korea ta Arewa mai suna Liu Xiao Ming ya ce, mika wutar yola a birnin Phingyang ya zama ziyarar samun nasara da jituwa cikin kyakkyawan hali tare da kwanciyar hankali kuma lami lafiya.(Halima)