Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-28 10:54:57    
Kawo cikas ga gasar wasannin Olympics ba zai samu karbuwa daga wajen jama'a ba, in ji sharhin Jaridar People's Daily

cri
Yau 28 ga wata, jaridar People's Daily ta kasar Sin ta bayar da wani sharhi mai lakabi haka "Yiwa gasar wasannin Olympics karan-tsaye ba zai sami karbuwa daga wajen jama'a ba".

Sharhin ya ce, gasar wasannin Olympics na dauke da fatan jama'a da burinsu a duk ilahirin duniya, tana kuma dauke da fatan duk duniya na samun zaman lafiya da cigaba. A cikin shekaru sama da 100 da suka gabata, gasar wasannin Olympics ta zamani ta riga ta zaman wani dandamali, inda kasashe daban-daban, da kabilu iri-iri, da mutane masu bin addinai daban-daban suke more kyawawan al'adu tare, da yin mu'amala tsakanin juna. Ko-ta-yaya danyen aikin da wasu 'yan tsirarrun mutane suka yi na kawo cikas ga gasar wasannin Olympics ba zai samu goyon-baya da karbuwa daga wajen jama'a ba. Kwanan baya, bi da bi ne shugaban kwamitin gasar wasannin Olympics na duniya Jacques Rogge, da mai bada shawara kan harkokin diflomasiyya na shugaban Faransa Jean-David Levitte tare da 'yan wasan motsa jiki na Amurka sama da 100 suka ki amincewa da saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics. A waje daya kuma, bikin yawo da wutar gasar wasannin Olympics ya samu cikakken goyon-baya daga wajen yawa-yawancin mutanen kasashen duniya daban-daban.

Sharhin ya kara da cewar, wadannan hakikanan abubuwa sun shaida cewar, gasar wasannin Olympics gagarumin biki ne ga daukacin mutanen duniya. Ko shakka babu, duk wani yunkurin kawo cikas ga gasar wasannin Olympics, da saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics ta Beijing, ba zai samu karbuwa daga wajen jama'a ba.(Murtala)