Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-23 10:01:53    
Kada a saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics ta Beijing, in ji kwararrun ketare kan hakkin bil'adama

cri
Jiya 22 ga wata, a wajen dandalin fadin albarkacin-baki kan hakkin bil'adama a karo na farko wanda aka yi a nan birnin Beijing, bi da bi ne kwararrun kasashen waje kan hakkin bil'adama suka yi jawabi cewar, kada a saka batun siyasa a gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Furofesa Sirrka Korpela ta sashen koyon ilimin dangantakar kasa da kasa na jami'ar Columbia ta Amurka ta ce, da gangan ne 'yan tsirarrun mutane suka kawo cikas ga bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics a wasu wuraren duniya. Wasu mutane suna son jawo hankulan duniya ta hanyar yin karan-tsaye ga bikin zagayawa da wutar gasar wasannin Olympics. Dangane da yunkurin saka batun siyasa a cikin gasar wasannin Olympics a kwanan baya, Korpela ta fadi cewar, wasannin motsa jiki da batun siyasa abubuwa biyu ne wadanda suka sha banban sosai. Ya kamata mutane su more da kuma halarci wannan gagarumar gasa, amma bai kamata ba a saka batun siyasa a ciki.

Wakiliyar koli kan hakkin bil'adama ta majalisar dokokin Ukraine Madam Nina Karpachova ta furta cewar, duk wani yunkurin kawo cikas ga gasar wasannin Olympics ta Beijing na da nufin yin shiga-sharo-ba-shanu cikin harkokin gida na kasar Sin. Ta kuma kara da cewar, kamata ya yi mutane su nuna adalci ga nasarorin da kasar Sin ta samu. Kasar Sin kuma za ta taka muhimmiyar rawa wajen daukaka cigaban zaman jituwa a duk duniya domin tinkarar kalubalen duniya.(Murtala)