Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 20:17:36    
A tsanake ne, kasar Sin ta yi adawa da a mayar da Dalai Lama matsayin ' 'dan birnin Paris mai daraja'

cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Jiang Yu ta bayyana a gun wani taron manema labaru da aka shirya a ran 22 ga wata a birnin Beijing cewa, a tsanake ne, kasar Sin ta yi adawa da majalisar dokoki ta birnin Paris da ta zartas da kudurin mayar da Dalai Lama matsayin ' 'dan birnin Paris mai daraja' a ran 21 ga wata. Madam Jiang ta ce, wannan aiki ya tsoma baki cikin harkokin gida na Sin, kuma ta lalata dangantakar da ke tsakanin Sin da Faransa.

Madam Jiang ta ce, mayar da Dalai Lama matsayin ' 'dan birnin Paris mai daraja' babbar tsokana ce ga jama'ar kasar Sin ciki har da jama'ar Tibet da yawansu ya kai biliyan 1.3, ya kara sa kaimi ga Dalai Lama da 'yan neman a-ware na Tibet.

Kasar Sin ta bukaci kasar Faransa ta dauki matakai masu amfani, domin kawar da mummunan tasiri sakamakon wannan lamari, da kuma daina nuna goyon baya ga 'yan a-ware na Tibet wajen kawo mata baraka.(Danladi)