Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 20:16:17    
Tsegumin da jami'in kasar Amurka suka yi wa harkar Tibet ta kasar Sin ya saba wa muhimmiyar ka'idar dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa

cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Madam Jiang Yu ta bayyana a ran 22 ga wata a birnin Beijing cewa, jami'in majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ya yi watsi da babbar adawa daga kasar Sin, ya gana da Dalai Lama, haka kuma ya yi tsegumi kan harkar Tibet ta kasar Sin, wannan ya saba wa muhimmiyar ka'idar dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa, ya tsoma baki cikin harkokin gida na Sin, wannan ya zama kuskure ne kuma bai dauki nauyin da ke bisa wuyansa ba. Kasar Sin ta riga ta yi fadi tashi da kasar Amurka.

Bisa labarin da muka samu, an ce, mataimakin sakataren harkokin waje na kasar Amurka Paula J. Dobriansky ya gana da Dalai Lama, kuma ya rubuta wani bayani a jaridar 'Washington Post' cewa, harkar Tibet ta bayyana matsin da gwamnatin kasar Sin ta yi wa addinin Tibet da al'adu da sauran 'yanci cikin dogon lokaci, yin shawarwari da Dalai Lama ya zama hanyar da ta fi kyau wajen daidaita matsalar Tibet.

Game da haka, Madam Jiang ta ce, rukunin Dalai Lama ya yi kulle kulle da kuma hada baki da rukonin neman a-ware na Tibet a ketare, sun tada tashe tashen hankula a birnin Lhasa a ranar 14 ga watan jiya. Kasar Sin ta bukaci kasar Amurka ta girmamawa hakikanan abubuwa, ta daina gudanar da ayyukan nuna goyon baya ga rukunin Dalai Lama wajen neman baraka ga kasar Sin, domin kada ta lalata dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Amurka, da kuma matsayin kasar Amurka.(Danladi)