Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-22 15:22:36    
Gidan ibada na Sera Monastery na birnin Lhasa ta sake fara yin aikace-aikacen addinin budda

cri
Bisa labari da aka samu, an ce, ran 20 ga watan Afril ita ran 15 ga watan maris bisa kalandar kabilar Tibet, kuma ita rana ce da aka yi aikace-aikacen addinin budda. Ran nan da karfe 10 da safe, masu bin addinin budda guda 380 na gidan ibada na Sera Monastery sun shiga babban dakin gidan ibada cikin lokaci, kuma sun fara yin aikace-aikacen addinin budda a karo na farko tun bayan aukuwar mummunan tashin hakali a Lhasa. Aikace-aikacen addinin budda da aka shafe awa biyu ana yinsu suna tafiya cikin lami lafiya.

A ran 18 ga wata, sakataren reshen Jam'iyyar Kwaminis ta Sin a jihar Tibet Mr. Zhang Qingli ya zo gidan ibada na Sera Monastery kuma ya yi tattaunawa da wakilan masu bin addinin budda, inda ya ce, tilas ne reshen Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da gwamnatin jihar Tibet su kare hakkin masu bin addinin budda na son kasar da kuma son addinin budda da kuma moriyarsu bisa doka, kuma samar da su wata kyakkyawar yanayin bin addinin budda.

Wani mabiyi addinin budda mai suna Losang Chosphel da shekarunsa ya kai 75 na gidan ibada na Sera Monastery ya gaya wa Mr. Zhang Qingli cewa, masu bin addinin budda iri na gaskiya ba za su yi abin laifi kamarsu fasa wurare da kwashe dukiyoyi da kuma cinna wa motici da gidaje wuta. Sun ji bakin ciki sosai, sabo da akwai wadansu mutane masu bin addinin budda sun shiga cikin lamarin "3.14" a Lhasa.

Bisa labari da aka samu, an ce, yanzu, gidajen ibada na birnin Lhasa sun sake fara yin aikace-aikacen addinin budda bi da bi, gidajen ibada kuma an fara bude su ga jama'a da mutane masu yawon shakatawa. (Zubairu)