Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 17:24:38    
Bayanin kabilar Miao

cri

Yawancin 'yan kabilar Miao suna zama a yankunan kudu maso gabashin lardin Guizhou da yankunan tsaunin Damiaoshan da lardin Hainan da wasu yankunan da ke bakin iyakar da ke tsakanin lardin Guizhou da Hunan da Hubei da Sichuan da Yunnan da Guangxi. Yanzu wasu daga cikinsu suna kuma zama a yankunan arewacin nahiyar Amurka da kasashen kudu maso gabashin Asiya. Jimlar yawan mutanen kabilar Miao ya kai kimanin miliyan 9, wato na daya daga cikin kananan kabilun da suke da mutane da yawa. Yawan 'yan kabilar Miao da suke da zama a lardin Guizhou ya kai kimanin miliyan 4 da dubu dari 3. Sakamakon haka, lardin Guizhou lardi ne da ke da mutanen kabilar Miao mafi yawa.

'Yan kabilar Miao sun dade suna zama a nan kasar Sin. Ana ganin cewa, a lokacin da da da, wani mutum mai suna "Chi You" da yake daya daga cikin nagartattun mutane uku na kakanin-kakanin Sinawa shi ne kakanin-kakanin 'yan kabilar Miao. A da, an raba 'yan kabilar Miao sassa uku, wato sashe na Jiu Li da na San Miao da na Nan Mai. A cikin litattafin tarihi na kasar Sin, an dade ana rubuta tarihin kabilar Miao. A lokacin da ake cikin daular Qing da ta Han a nan kasar Sin, yawancin 'yan kabilar Miao sun riga sun soma yin zama a shiyyoyin Wuling da Zangke da Yuejun da Ba da Nan. Tsirarrunsu sun yi kaura sun yi zama a yankunan da ke shafar kogin Liujiang da ke kudu maso gabashin lardin Guizhou. A lokacin da ake daular Ming da ta Qing a nan kasar Sin, 'yan kabilar Miao sun soma yin zama a duk fadin lardin Guizhou, musamman a yankunan kudu maso gabashin lardin Guizhou da kudancin Guizhou da kudu maso yammacin lardin da yankin Tongren, ya kasance da kauyukan 'yan kabilar Miao da yawa. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, musamman tun daga shekarar 1951, bi da bi ne aka kafa shiyyoyi da gudummomi da kananan hukumomi na kabilar Miao a yankunan da 'yan kabilar suke da zama.

'Yan kabilar Miao suna da yarensu, amma yaren da suke fadi a yankuna daban daban suna shan bambanci sosai. A da, 'yan kabilar Miao suna da yare kawai, amma babu haruffan yarensu. A farkon karni na 20 da ya gabata, a karkashin taimakawar wani mutumin Britaniya wanda yake yada addinin Kirista a lardin a wancan lokaci, an kirkiro haruffan yaren Miao. Amma ba a iya yada shi ba. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, an yi amfani da harffan Latin an kirkiro haruffan yaren Miao, yanzu ana amfani da irin wannan haruffai a yankunan 'yan kabilar Miao. Amma domin 'yan kabilar Miao sun dade suna zama tare da 'yan kabilar Han, yanzu yawancin 'yan kabilar Miao sun iya harshen Sinanci.

Tattalin arzikin yankunan kabilar Miao yana dogara da aikin gona, wasu kuma suna sana'ar gandun daji da ta kiwo. A da, an bi tsarin mulkin kama karya a yankunan kabilar Miao. Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, an aiwatar da jerin manufofin yin gyare-gyare kan tattalin arziki da zaman al'ummar kabilar Miao. Sabo da haka, yankunan kabilar Miao sun soma shiga sabon lokacin cigaban tattalin arzikinsu.

Yawancin 'yan kabilar Miao suna zama a yankunan tsaunuka. Sun yi amfani da katako lokacin da suke gina gidajensu. Ana kiran irin wannan gida "ginin da ke da kafafu". Irin wannan gini yana da hawa 3, a kan kiwon dabbobi a cikin bene na farko, iyalai suna kuma kwana a cikin bene na biyu. A cikin bene na uku, a kan adana hatsi.

Yawan ire-iren tufafin matan kabilar Miao ya kai fiye da 130, ana shan bambanci sosai a yankuna daban daban. Yawancin mata suna sanya gajeren riga da buji iri iri. Abubuwan adon tufafinsu suna da kyaun gani sosai. Haka kuma a kan zana furanni iri iri a kan tufafinsu. Bugu da kari kuma, 'yan mata su fi son sanyan kayayyakin ado irin na azurfa a kan jikinsu. Irin wadannan kayayyakin ado na azurfa suna da nauyi sosai. Amma tufarin maza na kabilar Miao na wurare daban daban ba su da bambanci sosai.

'Yan kabilar Miao suna mai da hankali sosai wajen da'a. Da isar baki, sai dai sun yanka kaji ko agwagwa domin bakuncin baki. Idan bako mai girmamawa ya zo daga nesa, da farko dai, 'yan kabilar Miao za su gayyaci baki da su sha giya. Lokacin da suke bakuntar baki, dole ne su sanya kyawawan tufafin da su kan sanya lokacin da suke murnar shagulgula. A waje daya kuma, su kan maraba da baki masu girmamawa da giya a kofar kauyensu. Matasan kabilar Miao suna neman soyayya su da kansu cikin 'yanci. Matasa su kan san juna a gun shagulguna iri iri. Lokacin da suke neman soyayya, samari da 'yan mata su kan rera wa juna wakoki.

'Yan kabilar Miao kabila ce da take kwarewa sosai wajen waka da raye-raye. Kuma tana da wadatattun ladabi, kamar su tsoffin wakoki iri iri. Ko a gun shagulgula, ko a gun bikin aure ko a gun bikin jana'izza, ana iya sauraran wakokin da suke rerawa. A waje daya kuma, lokacin da suke waka, suna kuma taka raye-raye, kamar su rawar Lusheng da ta gangar katako da rawar kujera da rawar biri. Yawan ire-iren raye-raye na kabilar Miao ya kai fiye da 40.

'Yan kabilar Miao suna da bukukuwa iri daban daban, kamar su Ranar 8 ga watan Afrilu da sabuwar shekara bisa kalandar kabilar Miao da bikin Lusheng da bikin 'yan uwa da bikin kwale-kwale na dragon. Bikin sabuwar shekara ta kabilar Miao bikin gargajiya ne da 'yan kabilar Miao suke girmamawa kakanin-kakaninsu da murnar girbi. Dukkan 'yan kabilar Miao da suke da zama a yankuna daban daban suna taya murnar wannan biki, amma har yanzu ba su da wata tabbatacciyar ranar murnar wannan sabuwar shekara. Su kan taya murnar ranar sabuwar shekararsu a wata ranar da ke tsakanin watan Oktoba da watan Nuwamba bisa kalandar wata ta kasar Sin. Mutanen kabilar Miao su kan tayar murnar sabuwar shekararsu sau uku, wato karamin bikin murnar sabuwar shekara da babban bikin murnar sabuwar shekara da kuma bikin murnar sabuwar shekara na karshe. Daga cikinsu, babban bikin murnar sabuwar shekara ya fi muhimmanci, 'yan kabilar Miao su kan shirya bukukuwa iri iri a cikin kwanaki 3 zuwa kwanaki 5 a lokacin da ake babban bikin murnar sabuwar shekara. Amma a wasu wurare, ana shirya babban bikin murnar sabuwar shekara har fiye da kwanaki 10. Wani mhimmin biki daban na kabilar Miao shi ne "ranar 8 ga watan Afrilu" bisa kalandar gargajiya ta kabilar. Ma'anar wannan biki tana shan bambanci a wuraren kabilar Miao daban daban. A wasu wurare, ciki har birnin Guiyang, babban birnin lardin Guizhou, ana murnar wannan biki ne domin tunawa da "Zhu Dinnong", wani jarumi ne na kabilar Miao na lokacin da wanda ya rasu a cikin wani yakin da aka yi a garin Guiyang. Lokacin da ake murnar wannan biki, jama'ar kabilar Miao da suka zo daga wurare daban daban sun sanya kyawawan tufafinsu sun taru a cikin birnin Guiyang, inda suke waka da raye-raye da wasan kwallo da dai sauran wasanni iri iri domin tunawa da wannan jarumi.

Bikin "Nulie", wato a kan kira shi "cin gangar zang", wani gagarumin biki ne na 'yan kabilar Miao da suke da zama a yankunan kudu maso gabashin lardin Guizhou. A kowane shekaru 13 da suka gabata, su taya murnar wannan biki. Wannan biki yana da kasaita sosai, kuma ya kan shafi dogon lokaci. A gun wannan biki, dubban 'yan kabilar Miao suke wasa da shanu, kuma suke rawar Lusheng har kwanaki 7 ko 9. Sannan kuma su yanka wannan sa domin nuna girmamawa ga wannan ganga. (Sanusi Chen)