Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 15:39:19    
Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Malaysia ya kira wata liyafa don maraba da wutar wasannin Olympic na Beijing

cri

A ran 20 ga wata, wato ranar da aka kai wutar wasannin Olympic na Beijing ta shekarar 2008 a birnin Kuala Lumpur, ofishin jakadancin dake kasar Malaysia ya kira wata liyafa ta gajeren lokaci don maraba da zuwan wutar wasannin Olympic a kasar.

Jakadan kasar Sin dake Malaysia Cheng Yonghua ya ce, mika wutar wasannin Olympic na Beijing a duniya, ya kawo wa duniya zumuncin jama'ar kasar Sin, ya watsa tunanin Olympic na zaman lafiya da zaman jituwa da hadin gwiwa da sada zumanta, kuma ya samu goyon baya daga mutanen duniya dake kaunar zaman lafiya da nuna goyon baya ga wasannin Olympic.

Shugaban kwamitin wasannin Olympic na Malaysia Punku Imran ya furta cewa, an riga an kammala aikin share fage ga mika wutar yula a birnin Kuala Lumpur.Ya ce, mika wutar wasannin Olympic a duniya ya kawo wa mutanen duniya farin ciki. A ganinsa, ko shakka babu, mika wutar yula a ran 21 zai kawo wa mutanen da suke son wannan aiki farin ciki sosai.

Za a fara mika wutar yula a ran 21 ga wata da karfe 2 da yamma. Babban jigon wannan aiki shi ne, "daga zamanin da zuwa yanzu", za a fara mika ta daga filin 'yancin kan kasa dake da dogon tarihi, za a wuce shahararrun gine-ginen Malaysia, a karshe dai, za a isa shahararrun tagwayen hasumiya ta birnin Kuala Lumpur.(Lami)