Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-21 14:57:22    
Mr. Gao Yunliang, dan kabilar Yi da iyalinsa

cri

Mr. Gao Jinfeng, dan Mr. Gao Yunliang shi ne ya gina wannan babban gida bayan da ya ware kudin Sin wato Yuan dubu 200. A shekarar 2000, Mr. Gao Jinfeng ya je garin domin koyon fasahar shuka ganyen lambu da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kuma ya bude wani lambun itatuwa na gidansa. Yanzu ya dasa itatuwa fiye da 300 wadanda ke ba da 'ya'yan da ake kira Longan, da itatuwan lichee fiye da 200 da wani irin itatuwa daban 180 a cikin lambunsa. Mr. Gao Jinfeng ya bayyana cewa, bayan da na shafe shekaru 4 ina aikin shuke-shuke, sai itatuwan da na dasa suka fara ba da 'ya'ya, yawan kudin shiga da na samu a waccan shekara ya kai fiye da Yuan dubu 40. Bisa matsayinsa na mutum na farko wajen koyon fasahar dasa itatuwa masu ba da 'ya'ya na kauyensa, Mr. Gao Jinfeng ya samu riba daga wajen aikinsa ya bayyana cewa,

"Wannan sabon gida wanda na gina shi ne musamman ta hanyar dogaro bisa kudin shiga da na samu daga wajen 'ya'yan itatuwan da ake kira areca da kuma hatsin da na sayar, matata kuma tana kiwon aladu, ban da wannan kuma na samu kudi da yawa daga wajen kayan lambun da na sayar a yanayin hunturu. Yawan kudin da na samu daga farkon watan Janairu zuwa watan Mayu na wannan shekara wajen kayan lambu ya kai kusan Yuan dubu 7 zuwa dubu 8, kuma na samu kudi kusan Yuan dubu 10 a shekarar bara wajen sayar da 'ya'yan itacen da ake kira areca."


1 2 3