Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-20 20:00:13    
Wasu kafofin watsa labaru da shahararrun manema labaru na kasashen waje sun kai suka kan labaran da kasashen yamma suka bayar ba bisa gaskiya ba

cri

A 'yan kwanakin baya, bi da bi ne, wasu kafofin watsa labaru da shahararrun manema labaru na kasashen waje suka yi intabiyu ko bayar da sharhohi, inda suka kai suka kan labaran da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka bayar ba bisa gaskiya ba dangane da tashe tashen hankula a jihar Tibet ta kasar Sin, haka kuma suka tattauna kan matakan kuskure da wasu mutanen kasashen yamma suka dauka.

Jaridar 'Rebelion' ta kasar Spain ta bayar da wani sharhi a ran 18 ga wata cewa, a halin yanzu, wasu kasashen yamma da kafofin watsa labarunsu suna kulle kulle da gudanar da wani kamfe domin mayar da kasar Sin a matsayin wata 'shaidan', makasudinsu shi ne domin hana bunkasuwar kasar Sin.

Tashar internet ta Jaridar 'The Korea Times' ta kasar Korea ta kudu ta bayar da wani sharhi daga Mr Tom Plate, professor na jami'ar UCLA kuma mamban hukumar kula da dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa da manufofin kasashen tekun Pacific ta Burkle na kasar Amurka, inda ya bayyana cewa, game da bukatar gwamnatin kasar Sin da ta jama'arta, CNN ta nemi gafara ne ba bisa sahihiyar zuciya ba. Sharhin ya jaddada cewa, ya zaman wata bukata da mutanen kasashen yamma suke da ita ta fara sanin kasar Sin, hakan zai iya yin mu'amala da juna.

Tsohon shugaban kamfanin dillancin labaru na kasar Mexico, kuma shahararren manemi labaru Mr Enrique Adolfo Aranda ya bayyana a 18 ga wata cewa, yau da watanni 8 da suka gabata, ya taba daukar labaru a jihar Tibet ta kasar Sin, labarun da wasu manyan kafofin watsa labaru na kasashen yamma suka bayar ba na gaskiya ba, matsayinsu ya saba wa ka'idojin watsa labaru na bisa gasikiya da adalci.(Danladi)