Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 21:39:37    
Ana maraba da baki da su je jihar Tibet domin raya ta

cri
A ran 18 ga wata, Ju Jianhua, direktan ofishin kula da harkokin waje na gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ya bayyana a birnin Lhasa, cewar jihar Tibet za ta ci gaba da aiwatar da manfufofin bude kofarta ga sauran yankunan duniya kamar yadda ta saba yi a da, kuma tana maraba da dukkan hukumomi da kungiyoyi da mutane wadandan suke da shirin taimakawa jihar Tibet wajen neman cigaba cikin sahihanci da su zuba jari da neman hadin guiwa a jihar.

A gun taron kara wa juna sani da aka shirya wa baki da daliban kasashen waje da wasu baki injiniyoyi da suke aiki a birnin Lhasa, Ju Jianhua ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Tibet tana mai da hankali sosai kan yadda za a iya koyon fasahohin zamani wajen fama da talauci da kiyaye muhalli da ba da ilmin tilas da kiwon lafiya da kiyaye al'adun gargajiya ta hanyar aiwatar da ayyukan hadin guiwa a jihar.

Amma a waje daya, ya jaddada cewa, gwamnatin jihar tana tsayawa tsayin daka kan matsayin nuna adawa da tsirarrun mutane da su yi amfani da ayyukan hadin guiwa domin aiwatar da ayyukan da ba su dace ba. (Sanusi Chen)