Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 19:30:20    
Ainihin burin rukunin Dalai shi ne neman maido da tsarin bautawa a Tibet

cri
Ran 18 ga wata, jaridar Guangming ta kasar Sin ta ba da wani bayani mai cewa, ainihin burin rukunin Dalai shi ne neman maido da tsarin bautawa ba tare da hakkin dan Adam ba.

Bayanin ya bayyana cewa, kafin shekarar 1959, jama'ar jihar Tibet suna shan wahalhalun tsarin bautawa na gargajiya maras tausayi. Tsirarun masu bin addinin Buddha da dattijai da kuma masu bayi sun ci da gumin bayin da yawansu ya kai misalin kashi 95 cikin dari bisa jimlar mutanen Tibet.

Bayanin ya kara da cewa, amma abu mai ban mamaki shi ne, wasu 'yan siyasa na kasashen yammacin duniya sun mayar da Dalai a matsayin wai wanda ke yin gwagwarmaya domin kiyaye hakkin dan Adam, a maimakon amincewa da abubuwan gaskiya, wato Dalai bai taba daina neman maido da tsarin bautawa a jihar Tibet ba. Ba su son daidaita kasar Sin bisa abubuwa yadda suke kasancewa, suna nuna goyon baya ga tsarin bautawa na gargajiya, wanda jama'a suka yi watsi da shi a tarihi.

A karshe dai, bayanin ya shawo kan wasu mutanen kasashen yammacin duniya da kada su fita cikin hankulansu. Dalai Lama yana gudanar da abubuwa ne da sunan wai kiyaye hakkin dan Adam, amma ainihin burinsa shi ne neman maido da tsarin bautawa a jihar Tibet.(Tasallah)