Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 16:54:52    
Sanarwar hukumar 'yan sanda ta birnin Lhasa kan mutanen da ake neman cafke su da wadanda suka kai kansu sakamakon shiga rikicin '3.14'

cri
A ran 18 ga wata, gidan TV na kasar Sin ya watsa wani labari game da yadda hukumar 'yan sanda ta birnin Lhasa ta sanar da yadda ake cigiyar wasu mutane ruwa a jallo da kuma mutanen da suka kai kansu sakamakon shiga rikicin ranar 14 ga watan da ya gabata.

Wakilinmu ya sami labari daga hukumar 'yan sanda ta birnin Lhasa cewa, ya zuwa yanzu, hukumomin da abin ya shafa sun riga sun ba da odar cafke mutane 170 sabo da akwai shaida cewa sun taba shiga tarzomar fasa wurare da kwashe dukiyoyi da kuma kone kayayyaki da ta wakana a ran 14 ga watan da ya gabata. Yanzu, an riga an kama mutane 82 daga cikin wadanda ake neman cafke su, 11 daga cikinsu kuma sun kai kansu don neman sassauta hukuncin da za a yanke musu. (Zubairu)