Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 12:52:05    
Kungiyar matasan kabilar Tibet tana canjawa daga kungiyar tada tarzoma zuwa kungiyar ta'addanci

cri

Jaridar People's Daily ta bayar da bayani a ran 18 ga wata cewa, kungiyar neman sauyi wato kungiyar matasan kabilar Tibet tana canjawa daga kungiyar tada tarzoma zuwa kungiyar ta'addaci.

A kwanakin baya, a matsayin shugaban kungiyar matasan kabilar Tibet, Tsewang Rigzin ya yi furucin ban mamaki a yayin da yake ganawa da wakilan kafofin watsa labaru cewa, "game da aikin neman 'yanci kan jihar Tibet, yin amfani da boma-bomai da aka daura a jikin mutane wata dabara ce." Amma tsohon shugaban kungiyar Kelzang Phuntsok ya ce "domin aikinmu, za mu iya tada tarzoma."

Bayani ya ce, bayan da aka kafa kungiyar matasan kabilar Tibet, kungiyar ta yi jerin kos na horaswa a fannin yakin sari-ka-noke da fasahar fashewa da sauransu; ta yi ta tada tarzoma; kuma ta kai naushi ga nakasasshiya mai mika wutar yula a gaban mutanen duk duniya. A cikin batun tashe-tashen hankula da aka yi a ran 14 ga watan Maris, ta kona farar hula da kantuna, kuma ta shirya bindigogi fiye da 100 da dubban harsashi da dubban kilogram na nakiyoyi, ta sanar da cewa, domin samun nasara a karshe, ta shirya "cigaba da kashe 'yan kabilar Tibet sama da dari daya."

Kazalika, bayanin ya bayyana cewa, ta'addanci abokan gaba ne ga zaman lafiya da bunkasuwar dan Adam. Amma tarzomar da kungiyar matasan kibilar Tibet ta kan samu goyon baya daga kofofin watsa labaru da 'yan siyasa na kasashen yamma, shi ya sa, kungiyar ta cigaba da tafiya a kan hanyar ta'addanci.(Lami)