Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-18 11:58:54    
"Babban taro na matasa na Tibet" ba ya da ikon wakiltar matasa na jihar Tibet, in ji shugaban kungiyar tarayyar matashi ta jihar Tibet

cri
Jiya 17 ga wata, a lokacin da manema labaru suka kai mata ziyara don jin ta bakinsa, shugaban kungiyar tarayyar matasa ta jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta madam Luo Mei, ta bayyana cewa, kungiyar da ake kira wai "Babban taro na matasa na Tibet", wadda daya daga cikin kungiyoyi masu neman "'yancin kan Tibet" na rukunin Dalai Lama, ba ta da ikon wakilatar matasa, da jama'ar jihar Tibet.

Madam Luo Mei, ita ce 'yar kabilar Tibet ce ta zalla. Ta ce, ko Dalai Lama, ko "Babban taron matasa na Tibet", dukkansu ba su ba da taimako kan bunkasuwa da zaman karko ga Tibet ba. Saboda haka, ba su da ikon zargi kan halin da jihar Tibet ke ciki, kuma ba su da ikon wakiltar Tibet, da matasan Tibet, da kuma jama'ar Tibet , don sanar da wasu manufofin siyasa da jama'ar jihar Tibet ba su amince da su ba a kasashen duniya.

Kwanan baya, a lokacin da babban sakataren da ke kula da aikin yin cudanya na "Babban taron matasa na Tibet" ya ke zantawa da manema labaru daga "Mujallar mako ta Asiya" ta Hongkong, ya bayyana cewa, wai "Babban taron matasa na Tibet" yana wakiltar moriyar jama'ar Tibet da gaske, kuma ya musunta shiryawa da halartar lamarin fasa wurare da kwashe dukiyoyi da kuma cinna wa motici da gidaje wuta a ranar 14 ga watan Maris a birnin Lhasa.

Madam Luo Mei tana ganin cewa, wannan kare baki ne kawai da 'Babban taron matasa na Tibet" ya yi, saboda ya musunta cewa, yana da nasaba da lamarin "3.14". Ta ce, lamarin ya kawo hasara sosai ga jihar Tibet, amma sun ce suna wakiltar moriyar matasa da jama'ar Tibet, wannan ne maras hankali. (Bilkisu)