Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-17 17:05:43    
Wani manomi mai fama da kwararowar hamada

cri

Jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta dake arewancin kasar Sin tana daya daga ciki jihohi da larduna da suka fi samun hamada mafi fadi a kasar Sin. Bisa kokarin da gwamnatocin kananan hukumomi da jama'arsu suka yi a cikin shekarun bayan baya, an samu babban ci gaba wajen yaki da kwararowar hamada a jihar nan. Daga cikin wadannan mutanen da suka bayar da taimakonsu wajen yaki da kwararowar hamada da akwai wani tsoho manomi da ake kiransa Gao Linshu wanda ya nace ga yaki da kwararowar hamada da dasa bishiyoyi cikin shekaru 19 da suka gabata, har ya bayar da babban taimakonsa wajen yaki da kwararowar hamada.

Tsoho manomi Gao Linshu yana da shekaru saba'in da haihuwa yana zaune a wani yanki dab da kogin rawayan kogi na kasar Sin da gwamnatin birnin Eerdos ta mallaka a kudu maso yammacin jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta. Fadin yankin da gwamnatin nan ta mallaka ya kai kusan muraba'in kilomita dubu casa'in wadda a cikinsa da akwai hamadar Maowusu da ta Kubuqi da fadinsu ya dau kashi 48 bisa dari na daukacin fadin yankin. Gidan Gao Linshu yana bakin hamadar Kubuqi. Ga shi a yau, bishiyoyi na kewaye gidansa, sai ka ce hamada ta bace. Sara-kuwa ta manomi Gao Linshu ta bayyana cewa bishiyoyi layi bisa layi da aka dasa sun kare gidanmu daga kwararowar hamada.

"Wannan nasara ce da mahaifinmu ya samu, ga shi a a yau hamada ta bace. A cikin shekarun kusan ashirin da yake fama da kwararowar hamada, na kan kawo masa abinci."

Kafin shekaru 19 da akwai wani kauye a wurin nan. Duk da kwararowar hamada da raguwar amfanin gona, shi ya sa manoman kauyen nan sun yi kaura. Gao Linshu ya waiwayo da cewa "A can da babu kome a nan sai hamada. Na gaya masu kula da kauye cewa ina so in gina wani daki a nan, sun ce me za ka yi a wannan wuri, ko za ka yi wasa ne!". A shekarar da ya tsungunar da iyalinsa a wannan wurin, ya cika shekaru 50 daidai, ya gina wani soro a hamada mai tazara kilomita biyar daga kauyensa, ya fara dasa ciyayi da bishiyoyi. Wannan matakin da Gao Linshu ya dauka a lokacin bai samu fahimtar mutanen kauyensa ma har ma iyalinsa ba ya amince da shi. Matar Gao Linshu ta ce " A wancan lokaci na yi adawa da shi. Ban amince da zuwansa a hamada, ko ina hamada take ba saura me ya yi a wannan wuri. Duk da haka mijina ya zo wurin shekara da shekara domin dasa bishiyoyi da ciyayi. Ba na sa kafa a hamda na yi watsi da ita."

Tsoho manomi Gao Linshu ya nuna karfin zuciyarsa ya yi watsi da adawa da sauran mutanen suka yi masa, yana ci gaba da aikinsa yana tsammanin zai yi iyakacin kokarinsa wajen samar da wata hanyar rayuwa ga jikokinsa kome zai faru.".

A shekara ta 1988, Gao Linshu ya kasha kudin Sin RBM yuan 20 ya saye kanana bishiyoyi da ake kira willow a turance da nauyinsu ya wuce kilo dari. Tare da 'ya'yansa maza guda uku ya kai bishiyoyin cikin hamda da babu hanyar tafiya a ciki inda ya dasa bishiyoyin daya bayan daya cikin yin biris da iska mai sanyi. Amma bishiyoyin da suka dasa sun mutu bayan rana daya kawai sabo da saiwoyin bishiyoyin sun fito a sanadin iska mai karfi, duk da haka ba su daina da aikinsu na tukuru ba sun ci gaba da dasa bishiyoyin. 'ya'yansa sun ba da nasu taimako, sara-kuwarsa ta kawo musu abinci. Da haka daukacin iyalinsa ya shiga aikin dasa bishiyoyi.

Matakin da iyalin Gao ya dauka ya jawo hankalin gwamnatin wuri da ta samar masa da kanana bishiyoyi da ciyayi da iri irin shuke dake iya jurewa fari ta yadda zai yi jarrabawa. Gao Linshu ya ce " Daga baya gwamnatin wurin ta ba mu iri iri na bishiyoyin willow da na alfalfa da sauransu. Na kawo su gida na suka su, daga bisani dukkansu sun mutu sabo da iska mai karfi. Daga baya na sami saiwoyin bishiyoyin reed, na huda gona na dasa su da dama. Na yi sa'a an yi ruwan sama bayan kwanaki goma sun rayu, na ci gaba da yin haka, bayan shekaru hudu, wurin nan ya cike da ciyayi masu yawa da tsawonsu ya kai sama da mita daya."

Daga bisani bishiyoyi da ciyayi da Manomi Gao Linshu ya dasa sun rayu. Fadin filayen da Manomi Gao Linshu ya dasa bishiyoyi da ciyayi a ciki ya habaka har ya wuce kadada metan. Tun farkon shekarun casa'in na karni da ya shige, gwamnatin birnin Eerdos ta jihar Mongoliya ta gida ta aiwatar da sabbin manufofin kiyaye muhalli na cewa duk wani manomin da ya dasa bishiyoyi da ciyayi a hadama shi ne ya ci moriyarsu, a sa'I daya kuma ta shigo da baki 'yan kasuwa da jari na ketare,ta yi kokarin bunkasa sana'o'in kayayyakin bishiyoyi da ciyayi, haka kuma ta kafa masana'antun yin katako da takarda cikin amfani da abubuwan asali na bishiyoyi da ciyayi, ta haka kuwa manoma da makiyaya sun samu karin kudin shiga ta hanyar dasa bishiyoyi da ciyayi. Tsoho manomi Gao Linshu wanda ya yi aikin tukuru cikin shekaru masu yawa ya ci gajiyar bishiyoyi da ciyayin da ya dasa a hamada. A shekara daya kawai kudin da Gao Linshu ya samu daga sayarwar kanana bishiyoyi ya kai kudin Sin RMB yaun sama da dubu ashirin, dadin dadawa, tare da ribar da ta ci daga sauran fannoni, kudin da iyalinsa ya samu ya kai kudin Sin RMB yuan dubu casa'in a shekdara daya. Wannan ba karamin kudi ba ne a wurin da manomi Gao Linshu ke zaune.

A shekara ta 1997, Gao Linshu ya gina wani gini mai dakuna hudu dab da bishiyoyi da itatuwa da ciyayi da ya dasa, duk iyalinsa ya zo wurin nan ya yi zama tare. Itatuwan poplar da ya dasa a kewayen harabarsa sun gima,tsawon wasun ya wuce mita goma. Iyalisan ya saye motar noma da ake kira tractor a turanci da kuma baskur da sauran ababan hawa. Da ganin manomi Gao Linshu ya samu wadata, wasu kauyawan da suka yi masa dariya a da, tunaninsu ya fara canza suna so suna koyonsa. Sun nemi Gao Linshu da ya koya musu yadda aka dasa bishiyoyi da ciyayin. Gao Linshu ya ce "Manoman dake cikin kauyenmu sun ga ci gaban da na samu a cikin 'yan shekarun baya, sun yi tattaunawa da ni kan yaya za su yi,sun ce suna so su dasa bishiyoyi da itatuwa, na gaya musu cewa kada su damu, zan ba su kanana bishiyoyi da itatuwa domin da akwai kanana bishiyoyi da yawa a karkashin manyan bishiyoyi nawa, ina so in samar da su ga manoman da ke cikin kauyenmu. Daga baya makwabatana sun fara dasa bishiyoyi da itatuwa, abin da ka iya yi,mu ma mu iya, muna so muna yakar kwararowar hamada, mu nuna kwazo da himma wajen dasa bishiyoyi da itatuwa."

A karkashin jagorancin manomi Gao Linshu, manoman na yankin nan sun fara yaki da kwararowar hamada suna dasa bishiyoyi da itatuwa da kuma ciyayi. Wani jami'in gwamnnatin wuri mai suna Huan Jianjun ya ce Yankin nan hamada ne kafin shekaru 19. mazaunan yankin nan sun sha wahala kwarai da gaske a zaman rayuwarsu. Bayan da gwagwarmayar da Gao Linshu da abokansa suka yi cikin shekaru 19 da suka gabata, an sami wani dausayi a cikin hamada. Gao Linshu ya ba da wani misalin koyo, manoma masu yawa suna so su bi sawunsa. A halin yanzu mutane masu yawa sun sane da cewa hamada ba abu mai ban tsoro ba ne, muna iya kyautata ta da muhalli ta aiki tukuru."

A shekara ta 2006, an daukaka manomi Gao Linshu a matsayin jarumi mai yaki da kwararowar hamada a yankin birnin Eerdos na jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin. Abu mafi farin ciki gare shi shi ne fadin filayen bishiyoyi da ciyayi ya karu daga kashi 20 bisa dari a da zuwa kashi 70 bisa dari na yanzu, fadinsu ya kai kadada miliyan daya da dubu dari uku da talatin a yankin birnin Eerdos bayan kokarin da suka yi cikin shekaru da dama, gonakai sama da kadada dubu dari hudu sun samu kariya daga zirin bishiyoyin hana kwararowar hamada. Cikin sinanci sunan Gao Linshu yana nufin babban daji ne. Ga shi a yau a ganin Gao Linshu burinsa ya cika ya dasa bishiyoyi da itatuwa da ciyayi masu yawa domin jikokinsa.

Jama'a masu sauraro,wannan dai ya kawo karshen shirinmu na yau na zaman rayuwar sinawa. Muna fatan za mu sake saduwa da ku a wannan lokaci na mako mai zuwa. Mun gode muku saboda kun saurarenmu .(Ali)