Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-16 20:26:05    
Ban da Dalai Lama na zuriya ta 14, Dukkan tsofin shugabannin masu bin addini na Tibet suna da al'adar kishin kasar Sin

cri
A kwanan baya, lokacin da yake ganawa da manema labaru, Mr. Xu Xingsheng, direktan sashen dab'in litattafin kabilu na wani kamfanin dab'i na kasar Sin ya bayyana cewa, dukkan tsoffin shugabannin masu bin addini na Tibet suna da al'adar kishin kasarsu da addinin da suke bi. Amma sai dai ba ma kawai Dalai Lama na zuriya ta 14 ba ya son kasa mahaifa ba, kuma ba ya son addinin da yake bi ba, har ma yana aikata ayyukan kawo wa kasar Sin baraka.

Mr. Xu Xingsheng, masani wanda ya kware sosai wajen yin nazarin tarihin addinai ya ce, a gaban kasar Sin wadda take samun karfi a kai a kai, kuma bayan da aka kau da tsarin mulkin kama karya da aiwatar da tsarin tafiyar da harkoki da kanta a jihar Tibet a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma lokacin da jama'ar Tibet suke samun kyautatuwar zaman rayuwarsu a kai a kai, har yanzu Dalai yana yunkurin neman 'yanci kan Tibet. Ko shakka babu, zai ci tura baki daya. (Sanusi Chen)