Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 21:25:09    
Zaman rayuwar manoma da makiyaya na jihar Tibet yana ta samun kyautattuwa a kai a kai a 'yan shekarun da suka wuce

cri
Tun 'yan shekarun da suka wuce, ta hanyar daidaita tsarin shuka da kiwon dabbobi, da kafa hotel na gidaje, da yin aiki a waje, da kuma samar da kayayyaki da motoci, da dai sauransu, yawan kudin da manoma da makiyaya na jihar Tibet suka samu yana ta karuwa, kuma zaman rayuwarsu yana ta samun kyautattuwa.

Shugaban jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta Mr. Qiangba Puncog ya gabatar da cewa, a yunkurin bunkasuwar tattalin arziki na jihar Tibet, fararen hula sun samu hakikanin moriya sosai.

Kullum gwamnatin kasar Sin na mayar da hankali sosai kan bunkasuwar jihar Tibet, a shekarar 2006 ta tsara manufofin nuna fifiko guda 40, don kara saurin bunkasuwar Tibet, a shekarar 2007 kuma, ta tabbatar da ayyukan shirye-shirye guda 180 na Tibet, wadanda suka hada da darajar kudin Sin sama da RMB yuan biliyan 77, don sa kaimi ga bunaksuwar tattalin arziki da zaman al'umma ta jihar Tibet. (Bilkisu)