Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-09 16:08:16    
Tashin hankalin da gungun Dalai Lama ya shirya ya haddasa hasarar da ta kai kudin Sin miliyan dari uku

cri

A gun taron manema labarun da aka shirya ran 9 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta Qiangba Puncog ya bayyana cewa tashin hankalin da gungun Dalai Lama ya shirya ran 14 ga watan Maris ya haddasa hasarar da ta kai kudin Sin miliyan dari uku.

A taron yada labaran da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya, Mr Qiangba Puncog ya bayyana cewa bisa sabuwar kididdigar da aka yi, an ce gidajen kasuwa da shagunan da aka lalata a birnin Lhasa sun wuce sama da 1300, daga cikinsu gidajen sayar da abubuwan kawa sun fi samun hasara, wasun sun yi hasarar kudin Sin Yuan miliyan goma ko ashirin.

Qiangba Puncog ya bayyana cewa gwamnatin jihar Tibet mai cin gashin kanta za ta biya diyya ga iyalan 'yan kasuwa da suka yi hasara a cikin wannan tashin hankali wajen buga haraaji da kudin hayar dakuna da jinya da kuma ba da taimako ga wadanda suka rasa dangi. A cikin shekaru biyu zuwa uku gwamnatin za ta ba su rancen kudi ba tare da ruwan kudi ba.(Ali)