
Ban da wannan kuma kwararrun kasar Chile sun bayyana cewa, cin abinci da shan abin sha yadda ya kamata ba kawai zai ba da taimako wajen rage yawan kitsen da ke taruwa a jijiya kawai ba, a'a har ma zai iya kiyaye nauyin jiki da kuma bugun jini kamar yadda ya kamata. Kuma kwararru sun ba da shawara cewa, ya kamata a kara cin abincin da ke kunshe da cellulose, kamar 'ya'yan itatuwa da kayayyakin lambu da wake iri iri. Ban da wannan kuma ya kamata a kara cin kifi da madara da kuma man zaitun.
Bugu da kari kuma, kwararru sun bayyana cewa, motsa jiki zai taka muhimmiyar rawa wajen kyautata lafiyar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa. Suna ganin cewa, ya fi kyau baligai su rika motsa jiki har rabin awa a ko wace rana, kuma ya kamata samari su rika motsa jiki kimanin awa guda a ko wace rana.
Game da motsa jiki, wani nazarin da kasar Japan ta gudanar ya bayyana cewa, wasu mutane matsakaita da tsoffi suna sabawa da tashi da wurwuri wajen motsa jiki, wannan wata al'ada ce maras kyau, wadda za ta iya kara hadarin kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini. Ta haka an kawar da maganar "tashi da wuri zai taimaka wa lafiyar jiki" da a kan fadi kullum.
1 2 3
|